@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Dukiya ta tasance mafi girma daga cikin abinda dan Adam ke burin mallakarsa a duniya, duk wanda ya same ta, to, za mu iya cewa ya sami kashi 50 daga cikin kashi 100 na abinda ake burin samu a rayuwar duniya, domin tana daga cikin ado na rayuwar duniya.
‘’ DUKIYA DA 'YA'YA ADO NE CIKIN RAYUWAR DUNIYA .......‘’
Sai dai ita wannan dukiya ba ta taruwa sai ta hanyoyi 5 kamar yadda Imam Aliyu A-Ridha (A.S )ke cewa:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
‘’ DUKIYA BA TA TARUWA SAI DA ABUBUWA BIYAR:TSANANIN ROWA;da
TSAWAITA AIKI;
da
KWADAYI ME RINJAYE ;da
YANKE ZUMUNCI;da kuma
FIFITA DUNIYA AKAN LAHIRA .‘’
(Biharul-Anwar, J:73, SH:138).
Daga cikin abubuwa biyar din nan za muga 4 ababan zargi ne, 1 ne abin so daga ciki. Amma shi ma'abucin neman tara dukiya ya kanyi amfani da duk wadannan hanyoyi.
TSANANIN ROWA:- Wanda ya kasance marowaci ba zai iya ciyarwa daga abinda yake samu ba, hatta Imfaqi ba ya bayarwa don kada abinda ya samu,ya lalace.
TSAWAITA AIKI:- Bai zama abin zargi ba, domin ta hanyar nema ake samu, sai dai kawai a kiyaye dokokin Allah cikin wannan aiki.
KWADAYI MAI RINJAYE:- Kwadayi kan sa mutum ya zama maroqi , duk abinda makwadanci ke da shi za kaga yana hangen abinda wani ke da shi komai qanqantar wannan abin. A ko da yaushe so yake a ba shi.
YANKE ZUMUNCI:- Shi ma abu ne na zargi, amma fa'idar mai yinsa gare shi shine, zai sami dama wajen nisantar da abin hannunsa ga dangi, wanda hakan ke taimakawa wajen qara taruwar dukiyarsa. Idan ka kuji dangi dukiyarka ta huta.
FIFITA DUNIYA AKAN LAHIRA:- Sanin kowa ne cewa duk wanda ya fifita duniyar sa babu abinda ba zai aikata ba don ya same ta.
ABIN LURA
Fadin cewa yanke zumunci na daga cikin abinda ke sa dukiya ta taru , hakan ba cin karo da hadisin Annabi (S.A.W.W )bane me cewa:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ ZADA ZUMUNCI YA KASANCE HANYA NA SHIMFIDAR DUKIYA .‘’
Mu munyi imani da wannan hadisi, amma da za ka tambayi me yanke zumunci shi zai ce ma sada zumunci na hana tara dukiya , domin ta hanyar sada shi ana qarar da abinda ke hannu.
Ashe dai abin imani ne (believe ).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Gda.
08137925034
~14th February, 2020.
Tags:
Taskar ilimi