Sufeto-Janar Na 'Yan Sandan Najeriya Ya Gurfana Gaban Majalisar Dattawa
Fabrairu 06, 2020
Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu
Rarraba
Dubi ra’ayoyi
WASHINGTON DC — Majalisar Dattawan Najeriya ta sha alwashin taimaka wa rundunar 'Yansanda ta kasa da ingantattun dokokin da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro, bayan ta share Sa'o'i hudu tana tattaunawa da Babban Sufeton 'Yansanda na kasa a sirrance.
Sufeto Janar Mohammed Adamu
Sufeto Janar na 'Yansandan Najeriya Mohammed Adamu ya gurfana gaban Majalisar Dattawan ne akan hauhawar rashin tsaro da, al'amarin da ya addabi fadin kasar baki daya. Sun kwashi sa'o'i 4 suna ganawar ta sirri. Bayan fitowarsa sai ya ce ya yi masu bayanin halin da kasa ta ke ciki game da tsaro sannan ya nemi a bada dama domin a kafa 'yansandan tun daga unguwanni. Ya na ganin hakan zai taimaka wajen rage yawan matsalolin da ake samu a harkar tsaro a kasar.
To saidai wadannan bayanai nashi ba su gamsar da wasu Sanatoci ba, a ciki har da Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba, wanda ya ce akwai kalubale da ake da shi domin kundin tsarin mulki bai amince da yin irin wadannan 'yansandan ba, amma shi kanshi ya fi amincewa da a yi 'yansandan jiha domin Majalisa za ta iya aiki akan kafa wanan maimakon 'yansandan unguwani.
Amma ga Mataimakin Mai Tsawatarwa na bangaren Marasa Rinjaye, Sanata Sahabi Ya'u ya ce har yanzu wanan batun na 'yansandan unguwanni shawara ce aka kawo, kuma majalisa ba ta riga ta amince ba tukuna, shi ya fi ganin shi a bangaren bai wa kananan hukumomi da Jihohi damar yin ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, wanda ya ce yin haka zai kawar da rashin ayyukan yi da ke sa matasa shiga halin ta'addanci.
Majalisar Wakilai ma ta gana da shugabanin hukumomin tsaro da suka hada da Shugaban Sojin Ruwa,da na Sojin Sama, da na Sojin Kasa, da shuguban hukumar tsaron kasa da kwamitocin kwararru a majalisar wakilanhar na tsawon sa'o'i biyar.

Tags:
Labaran Duniya