Shirin Kiwon Lafiyar Iyali!!!! Fita Na Daya (1)





Na shafin Ma'asumah Nigeria News Update

Tare da sakina Ahmad
M.N.U. 030

Zamani ya canza yanzu muna wani lokaci ne da zakaga da yawan iyaye mata basu damu sda shayar da jariransu ba, sai dai su basu madara ko kamu d.s.s. Wanda hakan back dai-dai bane, domin rashin shayar dasu din yana taka muhimmiyar rawa wurin gurbacewar tarbiyarsu, kamuwa da cututtukan yara.d.s.s

Shayarwa ga jarirai, wani Abu ne daba mutane kadai keyi ba, hatta wasu daga cikin dabbobima suna shayar da jariransu da zaran sun haihu. Bincike ya tabbatar da cewa shayar da jarirai nonon uwa a kasa da minti 30 da haihuwarsu yana kara masu lafiya, da kuzari, domin su jarirai a farkon rayuwarsu basa iya jurema wani abinci na daban inba nonon uwa ba.

Shayar da jarirai wani hakki ne da Allah (T) cikin hikimar sa ya dorama iyaye mata, haka yake ga mutane da dabbobi. Duk da yake an San cewa mutane da dabbobi na shayarwa, amma nonon mutum ya ban-banta dana dabbobi. Acikin ni'imar da Allah (T) yayima mutane shine ya sayara a nonon wasu dabbobin abin sha agaremu, kuma mai kyau kamar yadda yake fadi acikin littafinsa mai tsarki, cikin suratul (Nahl).
  Bincike ya tabbatar da cewa ba abinda yakai nonon uwa kyau ga jaririn da aka haifa. An tabbatar da cewa nonon uwa yana kunshe da duk abinda jariri zai bukata, dai-dai da yadda hanjinsa da gangar jikinsa zasu dauka ba tare da wani lahani agareshi ba. Likitoci da masana ilimin abinci sun tabbatar cewa shayar da nonon uwa nada fa'idodi dayawan gaske Wanda Allah (T) ya tanadar ga masu shayarwa da kuma abinda aka shayar.
Daga cikin fa'idodin shayarwa babu wani abinci mafi kyau da inganci ga jarir sama da nonon uwa. Shi nonon uwa shine kadai da yafi duk wani abinci inganci da daraja ajikin jariri tun daga haihuwarsu har zuwa wata 4 na farkon haihuwarsu. Aduk wannan lokacin babu abinci da za'abawa jariri dayafi nonon uwa kyau.
An tabbatar da cewa nonon uwa na tattare da duk abinda jariri ke bukata na rayuwar sa. Awannan lokacin harda isasshen ruwa da sinadarin gina jiki dana kariya daga cututtuka. Allah (T) mafi sanin bukatun jarirai ya sanya nonon uwa ya kasance wadatacce wurin biyan bukatun yara, madarar gwan-gwani bazai taba maye gurbin nonon uwa ba.



Daga cikin fa'idodin shayarwa akwai kare jarirai daga cututtuka. Likitoci sun lura da cewa jariran da basa samun shawarwa, sunfi saurin kamuwa da cututtuka irin gudawa, tari, da mura. Bincike ya nuna cewa lallai nonon uwa babban garkuwa ne daga kwayoyin cuta, don Allah (T) ya sanya sinadarin kariya acikin sa. Sannan shayarwa tana kara kawo kusanci a tsakanin uwa da yaro, batun kusanci tsakanin uwa da yaro awani al'amarine da Allah (T) ne kawai yasan hakikar dangartakar dake tsakanin su ( mahaifi da abinda aka haifa) acikin suratul (BALAD)
Idan muka lura zamuga cewa akwai ban-ban ci a tsakanin yaran da ake shayarwa da madara da kuma yaran da suka samu shayarwar daga iyayensu, a dabi'a da halayya. Rashin shayar da yara yana sa yara su taso marassa tausayi ga iyayensu bare sauran al'umma. Kangarar yara marasa daraja iyayensu a kasashen turai ance yanada nasaba da yawan shayardasu da madara ne amai makon nonon iyayensu.
Nonon uwa tushe ne na samun karfi da kuzari, da girma da garkuwa daga cututtuka ga jariranmu. Allah ya taimakemu mu sauke hakkin yara dake kawukanmu.

*Muhadu a mako na gaba don ci gaba da sauraron yadda zamu kare lafiyarmu data iyalanmu.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post