Jiya Laraba, Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya je ziyara garin Maiduguri ta jihar Borno, inda a al'ummar garin na Maiduguri suka tarye shi da ihun "Basu so! Basu yi!" gami da tofin Allah tsine da bayyana gajiyarsu a kan gazawarsa.
Ga alama wannan ihun da aka wa Buhari bai masa dadi ba, kamar yadda bai wa masoyansa ma'abota makaumiyar soyayya dadi ba, don haka Buhari na gama ziyararsa ya bar garin, kwatsam sai ga harin Boko Haram an kai a yammacin na jiya, wanda wasu suka kalli wannan harin a matsayin Kasheji ne ga mutanen Barno da suka wa Buhari ihun basa yi.
Wasu makafi masoyan Buhari sun ta rubuce-rubuce a Facebook, suna cewa ko dai yan Kwankwasiyya ne suka je Maiduguri suka wa Buhari ihun nan? Wani yace a'a, yan Shi'a ne suka taru suka masa ihun. A yayin da wasu suke cewa ai ba Buhari aka wa ihun ba, an ma Gwamnan jihar ne, Malam Zulum. Wasu kuma suka ce a'a Sojoji ake ma ihun, sune ba a so ba Shugaba Buhari ba.
Ko ma yaya ne, wannan duk borin kunya ne, domin Zulum ya saba zuwa cikin al'ummar jiharsa basu masa ihu ba. Su kuwa Jami'an tsaro kullum cikinsu ake rayuwa. Sai dai in kana nufin Buratai akewa ihun, wanda shi kuma abu guda ne da Buharin. Don haka Buhari suka ma ihu, kuma Maiduguri sun ba da sample ne. Ya kamata sauran gurare su sauki wannan samfurin in makashin bayin Allah, azzalumin bawa ya sake zuwa musu da nufin yaudara.
Kun ji kuma wai Shugaban sojoji yace ko an kore su ba za a dena Boko Haram ba ko? Wanda yake nufin koma wa za a kawo za a kawo shi bisa sharadin abin da ke gudana zai cigaba da gudana ne. Tunda daga sama ake gudanar da abin. A yayin da yake wannan maganar, shi kuma wani jami'in gwamnati na cewa suna kira ga Amurka ta zo ta kawo musu tsaro a kasa. Wanda yake nuna an kusa isa wajen, da zaran sun zo shikenan zance ya kare, za a fara ta'addancin ne na sosai.
To, duk ma ba wannan ba, a yayin da aka lura cewa mutane sun gane cewa jami'in tsaro bangaren Boko Haram, Shekau ya kai hari a kan mutane bayan da suka ce basu yin mai gidansa Buhari. Sai wai gashi Shekau din na wa Buhari Kasheji a kan kar ya sake zuwa Maiduguri, in ya sake zuwa za su gamu. Iskancin banza da hofi, gami da zunzurutun rainin wayau.
Boko Haram karya ce, ba wata tsiya Boko Haram, ba wasu mutane masu kishin addini da suke kokarin dawo da addinin Musulunci da suke kashe-kashen nan, gwamnati da Jami'an tsaronta ke yi. Su ne Boko Haram din ba wani ba. Su suke kashe kashen nan, kuma da wannan suke natsuwa a kan mulkin. Wannan tuntuni Jagoranmu ya fada mana, kuma muna gani kamar hasken rana.
In da gaske akwai wani abu Boko Haram, wai suna son rushe tsarin Nijeriya ne su kafa Musulunci, da'awa za su yiwa mutane su fahimce su ko kashe mutanen? In suka kashe mutanen su wa za su mulka bayan sun kafa daular kuma? Kuma a ina ake tafi da tsarin mulkin? A Maiduguri ko Kano, ko kuwa a Abuja? A ina Shugaban kasa yake? Ba Abuja ba? Me yasa ba su kai hari a Aso Rock, ko su kashe masu mulkin kasar, kullum sai kashe talakawa, musulmi da kirista, a masallatai, coci, kasuwa, tashan mota da kauyuka!?
Ana kera makamai a cikin Nijeriya ne? Ba daga waje ake shigowa da su ba? Ta ina ake shigowa da su alhali mai shigo da shinkafa ma ba a barinsa da ransa bare Bindigun da suke fin na sojin Nijeriya? A wace kasa suke sayo makaman? Wa ke biyan kudin makaman? Ta ina ake shigo da su har a kai musu? Ko a Sambisa suke kerawa?
Rainin hankalin ya isa haka! Ya kamata al'ummar Nijeriya su fahimci karatun nan, su fita daga rakiyar mutanen nan, a dena raina musu wayau, su fito su ce ba su yarda ba, a dena kashe su ana yin siyasa da rayukansu da sunan ana basu tsaro, alhali yaudara ce kawai ake musu.
Tags:
Labaran Duniya