🇳🇬Ma'asuma Nigeria News Update : tare da Isma'il Abubakar Idris Katsina
A Ranar Lahadi 09/Feb/2020 sheik Yaqub Yahaya wakilin 'yan uwa Musulmai Almajiran Sayyeed Zakzaky na Da'irar garin katsina ya bada wasu Shawarori ga masu amfani da (Social media) a wajen taron karawa juna sani na (Social Media) ta kasa wadda ta gudana a garin Katsina na yini biyu (2).
Sheik yana cewa "Mafi yawan 'yan Jaridu da na Social Media gurin su suyi batanci akan mu, kada Mutum yasha mamaki cewa wadan nan 'yan Social Media namu sune zasu zamo babbar ma'aikatar yada Labarai a Kasar mu ta Najeriya domin gidajen Rediyo, Talabijin, Jaridu, Kafofin sada zuminta gaskiya tayi karanci mafi yawan su basa cika fadin gaskiya".
Ya kara da cewa (Ya zama dole ga 'yan Social Media da su kara fahimtar Ka'idojin rubutu domin karin ingancin ayyukan su, ko wane dan Social Media ya rike aikinsa tsaninsa da Allah ya sawa kansa yakini akan aikinsa ya rika fadin gaskiya ga duk abin da zai rubuta, ya kamata 'yan Social Media su kara fadada tunaninsu).
Sheik yana cewa (Social media wata kaface wadda ake tallata gaskiya da karya aikinmu anan shine murika fadin gaskiya akan koma wanene, 'yan Media na Harka mukara karfi wajen bayyana ma Duniya akan Mazlumiyar da akayiwa Malam Zakzaky daga yanzu harzuwa karshen Duniya).
Ya kara da cewa ('Yan media su nemi tsofaffun Jawaban Malam Zakzaky surika amfani dasu wajen mai sanar da Al'umma ta hanyar Rubutawa, Audio, Bidiyo, a fassara ta ko wane yare ba Hausa da Turanci kadai ba!, a fassara Hausa, Turanci, Larabci, Faransanci da sauran yaren Duniya domin al'umma su amfana).