Cewar Matar Shaheed Alhaji Ibrahim Ahmad MD alheri block
🇮🇪Ma'asumah Nigerian News Update
Firar dasukai da wakilinmu
MJ'Matashi Ibrahim
WAKILINMU
Sunana MJ Matashi Ibrahim kozan iya sanin sunan malamar
SHAHEEDA
Sunana:- Shaheeda Alhassan
WAKILINMU
Kina wanne garine da zama
SHAHEEDA
Bauchi(misau)
WAKILINMU
zakikai shekara nawa yanzu
SHAHEEDA
Shekarata 22
WAKILINMU
Kina da aure
SHAHEEDA
Eh amma mijina yayi shahada a Zaria 2015
WAKILINMU
Amma zakukai shekara nawa da aure yayi shahada
SHAHEEDA
Watanmu Bakwai
WAKILINMU
Kafin kuyi aure dashi yana da wata matar
SHAHEEDA
Eh, yana da mata daya da yara (7)
WAKILINMU
Bayan kunyi aure wanna darasi kika dauka dangane da zama dashi dakuma ita abokiyar zaman naki dama yaranta
SHAHEEDA
To a zamana da Mijina wato Shahid, Zama mukayi wata bakwai Amma tamkar munyi shekara bakwai Shi wato tun bayanda mukayi aure Sbd irin tausayinsa garemu Kyautatawarsa, Ibadarsa, Kyauta, Hakuri Ga girmamawa hatta ga na kasa dashi Wannan dalilin yasa wasu lokuta nakan Kira Shi da 'Shahid.
Idan zaka cutar dashi sau nawa wlh bazai tamka ba Amma abinda ya shafi Addini bai daukesa da wasa ba Akwai wata kauna boyayya wadda yake ma Abba (H) Wadda bansan ya zan misalta a fahimta ba Wata Rana sai nayi mafarki, Ana program haka to Su ABBA (H) sune suke jawabai sai muka iso ni dashi a makare Sai muka fito a motansa muka shigo wajen program din ABBA na jawabi, sai na wuce bangaren sisters Wallahi billahi sai ABBA suka dakata da jawabin suka zo suka nuna masa inda zai zauna.
WAKILINMU
Agefe gudu yaza mantakewarki takama keda dayar matar tasa
SHAHEEDA
Dayake ba gida daya muke ba Dan haka bamu zauna tare ba sai bayan da akai waqi'a
Akwai kauna tsakanina da yaransa Mun shaku da diyarsa wacce ita ce auta ya tafi lokacin tana rarrafe Sunanta Sukaina, Ina matukar sonta, akwai shakuwa wadda Allah ya kimsa tsakanina da ita sosai
Ina kaunar mijina yana kaunata Azzaluman(Sad) Mamuguntan najeriya suka rabani dashi, Bazamu yafe ba da sannu sai mun dauki fansarku Habeybeee na
WAKILINMU
Amma idan akace miki mijinki yadawo ya zakiji aranki
SHAHEEDA
Bazan misalta ba Amma lallai sabuwar kyauta ce daga Allah Amma tabbas hakan shine farin cikina
WAKILINMU
Amma idan kika samu wani mijin zaki aure ko kwa kin hakura
SHAHEEDA
To wannan nufin Allah ne Amma idan a so nane na samu nawa rabon na riski mijina
WAKILINMU
To wanne kira zaki ga yan uwa mata wadand suka smu jarabawa irin taki
SHAHEEDA
To kirana garesu shine Mu sani kuma muji cewa yanzu ne zamu fara ita wannan gwagwarmaya dinKashe mazajenmu baisa mana rauni ba Face ya kara Mana izza da kumaji akan ita wannan tafiya din Yadda muke alfahari da mazajenmu kan hanyarda suka tafi to muna fatan suma mazajenmu suyi alfahari damu akan abinda suka barmu akai har zuwa ranarda zamu riskesu
WAKILINMU
Amma haryanzu kema kina da burin kitafi akan abin da yatafi
SHAHEEDA
Kwarai kuwa Shine babban burina tun bayan tafiyar ban saurara ba Ba Kuma zan tsagaita ba har sai mun cimma hadafi
WAKILINMU
Daga karshe wanne kira zaki gayan uwa
SHAHEEDA
Babban kirana abinda yafi damuna Muji tsoron Allah mu hada kanmu, domin rarrabar kanmu shine babban makamin jahiliyya da zasu yakemu Muyi aiki da iklasi musamu yardar Allah Mu dake mu jure hanyar akwai wahala Amma dadinta yana gaba
Fatan Allah ya tabbatar damu ya bamu sabaty Allah ya tausaya Mana Yaba ma bayinsa Lafiya ABBA da UMMA ZEENA Ya kwato Mana su dg hannun miyagun bayi
Allah ya karawa addininsa kariya ta musamman.
WAKILINMU
Muna godiya sosai dafatan koda gaba munkara nemanki zamusamu hadinkai kamar yau.
SHAHEEDA
Elahee Ajab nima ngd
Tags:
Taskar Ma'aurata