-Mlm Abubakar Nuhu Talatar Mafara
Shahid ISHAQ ya kasance Daya Daga cikin Yan uwa Tara da Sukayi Shahada a GARIN Talata Mafara Takwas daga cinkinsu Yan Nan Cikin Gari ne.
Daga Cikin su akwai Shahid Shehu Mai dala Wanda Shine Shahidi Na Farko a Garin Talata Mafara a shekarar 1996 lokacin Abaca (Waki ar Yar Kofa). Shidai Shahidin(Shahid Shehu Mai Dala) Ba sananne bane a Cikin Yan Uwa Don ko Anan Daira ba kowa ya San Shi bah bai cika Shiga mutane ba, Ya kasance Yana da Aure kma ALLAH swt)ya azurta Shi da samun Diya gda wadda ma tayi Aure Har Tana da Yaya biyu(Suhaila Shahid Shehu)
Shima ISHAQ ya kasance kamar Shahid Shehu ta bangarori da dama koma ince duk kusan Rayuwar su tazo Daya.
Ya kasance Daya Daga Cikin Zakakuran Matasa(Muballigun) tunda ya kasance Dalibi Mai Neman ilmi yayi karatun sa Anan Kulliya Inda ya Karanci Arabic kuma Yana daga Cikin Yan Uwan da suke karatu a Gurina Dan Haka mutane da dama Basusan Yana Aikin Jarida Bah don Nima ban san Yana wannan Aikin ba Saida aka halbe Shi bayan Su Hussaini da suka zo daga Funtua tare da Yan media Na Nan Garin Talata Mafara suka je gidan su Jaje to a wannan lokacin ne nake samun lbrin Dan Jarida ne, Don Haka Inbakayi Hulda dashi bah Baza ka Sanshi bah sai anyita maka misali kafin ka iya Gane shi.
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Dan Haka irinsu Shahid Ishaq basuda yawa a Cikin Al Umma, Ya kasance Yana bada gudummawa sosai Amma ba a Taba samun sa da wata Rigima Tsakaninsa da wani Dan Uwa bah.
Hakika Munyi Rashin Dan Uwa Hazikin Matashi Amma idan mukai duba da wata Fuska Zamu ga Cewa Babbar Nasara Ce aka Samu.
Kamar yanda nake fada Tun kafuwar Wannan Garin Ba a Taba Samun Shahidi bah ko a lokacin Shehu Usman Dan Fodio Babu Shahidi Anan Garin Talata Mafara.
Kma Sheikh Abdullahi Mai Gwanda yayi rubuce rubuce da dama kamar ko Acikin littafinsa(Tazyinil Warakat) yayi bayani dangane da Garin Na Mafara.
Amma duk lokacin Dan Fodio ba a Samu wani Da aka ce Gashi yayi shahada ba A Cikin Mafara, Kai ko malaman Jihadi bamu da anan Garin Talata Mafara sai dai malaman Fada.
Amma Albarkacin wannan Tafiya da Allamah Sayyid Ibraheem Zakzaky yakewa Jagoranci sai ga mu da shahidai Kai Harma da malaman Jihadi wannan kma ba karamar Daukaka Ce bah a garemu.
Shi Shahid Shehu Usman Mai Dala Kabarin sa Na Nan a Makabartar Gandu Amma su sauran Bakwai mun Samu Gangar Jikin Daya Daga Cikin su Wanda Kabarin sa Na Nan Darurrahma sauran kma Muna saran Suna Cikin Yan Uwan da aka Rufe a Mando(Mass Grave). Wannan Daukaka ce.
Kuma Shi Shahidi Yazo acikin Hadisi Cewa zai yi ceto a Ranar Alkiyama zai ceci mutum 70 ta bangaren ma haifi da Kuma mutum 70 ta bangaren mahaifinsa.
Dan Haka Mal yayi bayanai MASU yawa dangane da shahidi da kma Shahada Inda Kuma Mal ya Kara kawo wani Hadisi daga Manzon Tsira ya KE cewa da za a je wurin yaki a kashe ya sake dawo a sake kashe shi...Sannan yakoma Aljanna ya yaga Matsayinsa...
Yaci gaba da cewa Shahidi ya Na da daraja ta uku a Cikin jerin masu Daraja in da ya kawo su 1.Sune Annabawa da Mursalai 2.sune Siddiqai(a. Hiskilu, b. Habibu Najjar, c. Sai Kuma Imam Ali as) Sai Kuma masu Daraja ta 3. Sune shahidai sai kma ta 4.Sune Salihai.
Alhamdulillah Gashi Garinsu kauyene Amma Allah ya bashi Darajar da kowane Mutum yake so. Dan Haka Shahada ba karamar Daraja bace.
Daga Nan kma Mal ya yabama Aikin Jarida sosai Inda yace ba karamin Aiki bane yada Labaru na Yanar gizo.
Sannan Kuma Mal ya Kara encouraging dinmu akan Aikin da muka doru Akai yayin da ya bada misalin Hirarsu da waya da tsohon Kwamishina...
Daga karshe Mal yayi Nasihohi daga karshe Kuma akai Addu a.🌹
🌹Wassalamu Alaikum Was Rahmatullahi wa Barakatuhu🌹
😭😭😭
SHEIKH ABUBAKAR NUHU(ABBA) ya kasance Wakilin Yan Uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky dake Garin Talata Mafara, yayi Wannan Jawabinne lokacin Da wakilan Shafin Ma`asumah Sukakaimasa Ta`aziyyar Jajantawa da rashin Wakilinsu Daya da akayi .
Tags:
Game damu