@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
UMAR BN KHADDAB YA SHAIDI IMAM ALI (A.S )KAN HAKA
Wannan abu zai iya zama qalubale ga alqalai masu zartar da hukunci ko kuma maluma masu fitar da fatawa.
Haqiqa sanin ilimin alqur'ani na badini ba zahiri ba shi zai fitar da mutane daga fadawa cikin halaka, domin rashin sanin nasa zai iya yin jagoranci ga mutum wajen zartar da hukuncin da zai maishe shi azzami ta hanyar zaluntar wanda bai da laifi (innocent ).
Idan ka nazarci wasu hukunce-hukuncen da ake zartawa za kaga rashin sanin haqiqanin ma'anar ayoyin alqur'ani ne kawai ke jagorantar masu yin wadannan hukunci.
Don ka karanta tarjama ko kuma ka jibinci wasu maluma ba zai zame maka hujja ba, domin ba kowanne malami ne yasan ma'anar ayoyi ba, kuma hakan ma ta faru cikin wadanda aka riqa saukar da ayoyin a zamaninsu.
Jibintar Ahlul-Bait (A.S )ko wadanda suka sha daga gare su ne kadai zai iya tseratar da kai daga fadawa cikin halaka.
Bari mu kawo wanin hukunci da ya faru a zamanin Ibn Khaddab don daukar darasi.
MACE MAI CIKI DA TA AIKATA ZINA
Abinda muka sani na hukunci kan muhsini da ya aikata zina shine kisa (RAJAMU ), amma ba a kowanne irin yanayi ake zartarwa mutum hukunci.
Wata mata mai ciki ta yi zina a zamanin mulkin Ibn Khaddab, sai Umar din yayi umarni da a jefe ta. Sai Imam Ali (A.S )yace:
‘’ Sai kayi hankali,da abinda ke cikinta, domin fadin Allah (T )
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KUMA WATA RAI (mai laifi )BA TA 'DAUKAR LAIFIN WATA .‘’
(AN'AM, AYA TA 164).
Sai Umar yace, ‘’ Ban taba ganin wata matsala wacce baban Hassan ba zai iya warwareta ba. To, ya zanyi kenan?‘’
Sai Imam (A.S )yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KA KULA DA ITA HAR SAI TA HAIHU. IDAN TA HAIHU KA SAMI WACCE ZA TA SHAYAR DA YARON NONO, SANNAN KA YANKE MATA HADDI .‘’
(KITABUL-IRSHAAD NA SHEIKH MUFID )
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~24th February, 2020.
Tags:
Ahkamul islam