Daga: Wakilin mu, Bin Haroun Sigau tare da Ma'asumah Nigerian News Update.
Ko wanne ya ɗauki wajen da yaga zai bada gudunmawar sa don ganin an ƴanto Sayyid Zakzaky (H) wannan abun ko da zaka dauka koda zaiyi silar rugurgujewar duniyar ka baki daya. Rasa dukiya, rai, lokaci, fita struggle ne kowa yayi iya maƙurar abinda zai iya, kuma yake da yakinin shine makurar abinda yakamata yayi matsayin sa na mabiyin Sayyid (H).
Da yawan wasu zaka gan suna kokari iya kokari wajen hakan, amma abin tambayar, kai wanne hubbasa kayi ta janinbin ka? Me kake kuma wani planning kayi don bada taka gudun mawar. Akwai wadanda basu da halin zuwa Abuja, sabila da rashin kudi kai kuma kana dashi bakaje ba, baka kuma ba masu zuwa gudun mawa ba. A haka kake kiran kanka mabiyan Zakzaky?
Inda mahaifin ka ne yake wannan halin da Sayyid yake ciki, zaka barshi hakanan? Ko baka fada ba nasan bazaka bari ba sai inda karfinka ya kare. To, in mun manta barin tuna mana, Zakzaky yafi uwarmu yafi ubanmu don haka wajibi ne mu ƴanto sa kamar yadda nuke cewa Labbaika ya Rasulullah, Labbaika ya Husain da sauran A'imma to, shi Zakzaky wakilin su ne a doron kasa.
Don haka ko wannen mu yaji cewa Addinin Allah zai ceto, yayi iya yin sa don bada tasa gudunmawa. Kaji kamar ma Imam Husain (As) ne aka kama zaka yanto shi a matsayin ka na mabiyin addinin kakansa. Wallahi Allah hakki ne akan mu mu ƴanto Imamu kuma muddin muka gaza, Manzon Allah saiya tuhume mu gobe kiyama bisa barin mai tajdidin addinin sa cikin wanga hali.
Mu tashi/ki tashi kumu haɗa karfi da karfe har sai sun saki Imamu Zakzaky da dukkan yan uwan mu. Wannan ne kawai mafita garemu, Shehu shine kadai wanda ya san hanyar Manzon Allah (S) ta haƙiƙa ya zamu zauna zaman jangwam muna jira? shin wasu ne kenen zasu kwato mana shi?
Abin kunya ne gare mu, muna kwanciya waje mai kyau muci mai kyau, amma shugaban mu yan cen ko Oho! Wannan wacce irin biyayya kenen muke wa Sayyid? Mune fa kullum Sayyid ke kara karfafa mu kan nemawa duk wanda ake zalunta ƴanci, ko kun taɓa jin an zalunci wani Sayyid yayi shiru? Sai gashi mai ƴanta mu mun kasa ƴanto shi, wannan alamu ne na karatun da ake koya mana kullum baya shiga kwakwalen mu. Ko kuma yana shiga ɗin amma mun kasa saka shi a aikace.
Ina kira da babban murya ga wannan gwamnatin zalunci da su sake mana Jagora. fatan Allah ya ƙara wa Sayyid Da Malama Lafiya da nisan kwana ya. Ya kuma cika wa Sayyid burin sa na ganin addini yayi iko damu a wannan nahiya dama Duniya baki ɗaya.
#DeathToIsrael
#DeathToAmerica
#FreeZakzaky
#FreeUmmaZeenah
@Bin Haroun Sigau
Tags:
#FREE_ZAKZAKY