Rauhani: Takunkumin Amurka Ya Yi Kama Da Corona Tsoron Kamuwa Da Shi Ya Fi Hadarinsa Yawa

shugaban kasar Iran ya bayyana cewa Amurka tana barazana da takunkumi amma kuma sau da yawa ya kan zama dama ga kasashe domin dogara da kansu.

{maasumah.com.ng } (ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya gana da ministan harkokin wajen kasar Austria Alexander Schallenberg a yau a fadarsa da ke birnin Tehran.

A yayin ganawar, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, kasashen Iran da Austria suna da alaka ta tarihi, wadda ta ginu a kan girmama jina da kuma yin mu’amala da juna a bangarori daban-daban na ci gaba a tsakanin kasashen biyu.

Ya ce babban abin takaici ne yadda wasu kasashe suka dauki salon siyasar kakaba takunkumi kan wasu kasashe a halin yanzu saboda dalilai na siyasa, wanda hakan ya zama shi ne siyasar Amurka a yanzu, matukar wata kasa bat a mika wuya ga manufifin siyasarta ba, to za ta kakaba mata takunkumi, wanda hakan a cewar Rauhani ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa.

Ya ci gaba da cewa, dangane da batun yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar kasashen turai ba su cika alkawullan da suka dauka wa Iran ba, a kan haka Iran za ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniyar ne kawai daidai da yadda su ma suka mutunta ta.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Austria Alexander Schallenberg , ya bayyana cewa, kasarsa tana nan kan bakanta na mutunta yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da kasashen duniya, kamar yadda kuma alaka tsakanin kasashen biyu tana nan daram.

Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post