Nakhala: Za Mu Mayar Da Martani Idan Aka Yi Shishigi Kan al’ummar Palestine


Nakhala: Za Mu Mayar Da Martani Idan Aka Yi Shishigi Kan al’ummar Palestine

KARANTA QARIN WASU LABARAI ANAN
(MAASUMAH.COM.NGShugaban Kungiyar Jihadul-Islami Ta Palasdinu Ya Bayyana Cewa: Za Su Mayar Da Martani Mai Tsanani A kan Duk Wani Hari Na Isra’ila.

Ziyad Nakhala wanda ya gabatar da jawabi ga taron karawa juna sani na kasa da kungiyar Jihadul-Islami ta gabatar a birnin Gaza, ya ce; Duk wani wuce gona da iri na ‘yan Sahayuniya zai fuskanci mayar da martani mai tsanani maras tamka.

Nakhala ya kuma ce; Babu wani mahaluki da zai iya aiwatar da yarjejeniyar karni, da kawar da hakkokin palasdinawa, sai idan an kawo karshen gwagwarmayar al’ummar Palestine.

Babban magatakardar kungiyar ta Jihadul-Islami ya kara da cewa; Babu yadda za a iya karkatsa palasdinu zuwa yanki-yanki, sannan kuma ya kara da cewa; siyasar kisan gilla da ‘yan sahayoniya su ke aiki da ita, ba za ta sa Palasdinawan su kyale hakkokinsu

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


 salwanta ba.

Har ila ya, Nakhala ya yi hasashen cewa, jayayyar da ake yi a fagen siyasa za ta sauya zuwa filin dagar yaki a kowane lokaci.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post