Shugaban kasar Najeriya genar Muhammadu Buhari ya ce ya zuwa yanzu ya cika dukkan Alkawurran da ya daukarwa ‘yan Najeriya game da batun tsaro tun kafin ya zo mulkin Najeriya a shekarar 2015.
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Buhari ya fadi a hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ya ce “Na yi alkawarin kawo karshen ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram, garkuwa da mutane da sauram dukkan ayyukan ta’addanci da suka dabaibaye kasar mu Najeriya.”
Shugaban, ya kuma kara da cewa “Na san kowa zai yarda da abinda na fadi cewa nasarorin da muka samu ya dawo da girma da kuma kimar kasar mu Najeriya a idon duniya, haka kuma ina so na yi godiya ga ‘yan Najeriya bisa yarda da suka yi da gwamnatin mu.” A cewar shugaba Buhari.
Tags:
Labaran Duniya