Mun Lakuci Hancin Alƙali Ne...!!




-MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE.

Dubun-dubatar al'umma ne sukayi tagwayen muzaharori a tsakiyar garin Kaduna, sun fito ne domin kara jaddada kiransu ga gwamnatin Nigeria data gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy daga haramtacciyar tsarewar da take masa ba bisa qa'ida ba,

Kana da lakutar hancin alqalin da aka dorawa alhakin gabatar da shari'ar da gwamnatin jihar Kaduna ke ikirarin ta shigar da kara a gaban kotu a jihar ta Kaduna da cewa lallai kotun ta tabbatar tayi abinda ya dace kan lamarin.

Tagwayen muzaharorin dai an fara sune daya daga liventis round about daya daga Katsina round about duk akan titin Ahmadu Bello way dake tsakiyar garin Kaduna, muzaharorin dai sunyi kajibis da junane a dai-dai layin Kano road kana suka shiga cikin layin suka gangara suka rufeta a layin bayajidda street by Kano road.


A yayin da wakilinmu yake ganawa da wani cikin mahalartan yace lallai wannan muzaharar tamu muna bugun teburin alqali ne da karfin gaske da cewa lallai wajibin kotune ta tabbatar tayi abinda ya kamata kada tayi abinda bazai haifarwa da kasa da wannan jiha 'da mai ido ba.

Aiko suna da ikon yin zanga-zangarsu, kuma ai 'yancinsu suke nema, dokar kasa kuma ta basu dama, kuma lallai wajibine ayi musu adalci kamar yadda ake ikirarin anayiwa kowa-da-kowa domin suma 'yan kasa ne. (A yayin da wakilinmu yaji wasu'yan kasuwa na zantawa kenan a tsakanin su).

Sun fara tagwayen muzaharorin ne dai da misalin karfe sida na yamma 06:00pm, kuma sun farata lami-lafiya sun kammala lami-lafiya.

-Jabeer Bin Said Al'ansariy.
-MNU 016.
-05/02/2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post