Daga Ma'asumah Nigerian News Update.
Sayyid Zakzaky(h) shine mutumin da yayi gwagwarmawa wajan raya al'amuran Ahlul-Bayt (a.s) a wannan kasa tamu dama makota. Daga cikin baiwar da Allah Ya yi masa akwai samun nasarar maishe da ranar haihuwa Sayyada Zahra a matsayin Ranar Mata.
Zuwa yanzu, kusan shaikaru arba'in 40 kenan, Malam Zakzaky da al'amajiransa suna raya wannan rana ta 20 ga watan Jimada sani (ranar haihuwar Sayyada Zahra(a.s). Tun ana gabatar da taron cikin gomomi har ya zama dururuwa tafi-tafi har ya kai dubunnai, sai gashi yanzu taron ya gagara kidayar dubunnai saidai miliyoyi. Duk taruwan al'ummar da suke tunawa da wannan rana, shin kasan bayan wa suka rufa ?
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Malama Zeenat uwar gidan Shaikh Zakzaky(h) itace ta fara raya wannan rana ta haihuwar Sayyada Zahra a tarihin wannan nahirya tamu. Sabida haka duk wata mace da take tunkaho ko alfahari da kasancewarta ta masoyiya ga Sayyada Zahra to bayan Malama Zeenat zata take, kuma da bazarta take rawa, koda ba a so ba! Sabida haka raya ranar mauludin Sayyada Zahra yana daga cikin sunnonin da Malama Zeenat ta sunnanta bisa koyarwar Mijinta Shaikh Zakzaky. Allah Ya saka muku da mafi kyawun sakamako.Alfarmar wacce aka haifa a rana mai kamar ta yau 20 ga watan Jimada sani, Allah Ya gaggauta sakawa wadanda dominsu ne muka san kimar Darajar Annabi da Ahlul-Bayt har muke raya al'amuransu. Allah Ya gaggauta kwato mana su tare da sauran yan uwanmu daga hannun azzalumai, sannan Ya kaskantar da rayuwar azzalumai da masu goyon bayansu a nan duniya da can lahira.
- Abbakar Ibraheem Kudan.
20/06/1441
14/02/2020.
Tags:
Munasabobi