MALAM YAKUBU MAI HALIN ANNABAWA 5

MALAM YAKUBU BAWAN ALLAH (2)

@ma'sumah Nigerian news 

Update abbagano✍


Imam Khomeini yana cewa
أولئك العلماء هم مظهر الاسلام، انهم مبينو القران،انهم مظهر النبي الاكرم.

Wadan nan malaman sune suke bayyana addini,kuma lalle sune suke bayyana alkur,ani,kuma sune suke bayyana annabi.

Taudihi:

Su malam yakubu sune suke bayyana addini,domin daka gan su kana tuna addini, kuma tabbas dakagan shi,zaka gane abinda Allah ya saukar lalle yayi,kuma su malam yakubu sune idan kagan su zaka ga zahirin annabi.

Sune fa akace magada annabi Muhammad (s)
العلماء ورثة الانبياء.ومن جالس العلماء فقد جالسني ومن زار العلماء فقد زارني..

Annabi dakan sa yace idan ka zauna da su malam yakubu,kamar kazauna dashi ne,hakanan idan ka samu damar ziyarar su, kamar annabi ka ziyar ta.

Tabbas idan kazauna da su malam yakubu,to zaka kara gaskata maganar nan ta imam aliyu dayake cewa:

{جالس العلماء يزدد علمك ويحسن أدبك.
Babu yadda zaka zauna da su malam yakubu ace baka kara samun ilimi ba.kuma zaka kara kyautata halayen ka.saboda kazauna da wadan da ganin su kesa a Tina lahira.

(انما بخشى الله من عباده العلماء)

MALAM YAKUBU BAWAN ALLAH (3)

Tabbas wannan bawan allah, da kagan shi,lalle ka tabbatar kaga na Allah .

Kuma daka ganshi kaji zuciyar ka tayi dadi,mutukar zuciyar ka akwai digon imani.

Amman kuma wannan zamanin da muke ciki ko  Kuma wannan yanayin da muka shiga na rashin jagora a cikin mu.  Hakan yajawo wasun mu suke kokarin fitinuwa,se kaga yanzu yan'uwa bama yarda da malaman da su sayyed suka zauna  dasu lami lafia.

((سيأتي زمان على أمتي يفرون من العلماء،كما يفر الغنم عن الذئب،ابتلاهم الله تعالى بثلاثة أشياء.)
 ١. يرفع البركة من أموالهم.
٢.سلط الله عليهم سلطانا جائر.
٣.يخرجون من الدنيا بلا إيمان.

Lalle idan bamu guji kaucewa taba irin su malam yakub ba,to lalle Allah yana iya dauke albarka garemu,ko ya jarrabe mu da shuwagaban ni magwaye,ko a karshen rayuwar mu a cire mana imani..

Amman bawai nace malam yakubu baya laifi ba,tabbas shi bawai ma,asumi bane,yana iyayin laifi,Amman hakan se ya nuna ba malami bane??

Tabbas malam yakubu mumini ne na sosai,
Lokacin danaji yace ya yafewa duk Wanda yayi masa laifi da Wanda zai yi masa anan gaba.

Wannan ai se malamai.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post