Al’umma sun dauka cewa Buhari shine wanda zai cecesu daga halin kunci da suke ciki na rayuwa, hakan ya sanya su kasa su tsare har gogan nasu ya sami mulki, sai gashi an share sama da shaikaru biyar amma har yanzu babu wani ci gaba da aka samu, kullum saidai ci baya, har zuwa yanzu al'umma bata fita daga cikin halin qunci da kaskanci ba amma duk da hakan wasu basu fahimci cewa Buhari ba zai iya tsinana musu komi ba.
Ba komi ya janyo wannan ba illa sakin hanyar Allah da akayi da kuma daukan wanin Qur'ani a matsayin ma'auni na hukunci da kuma bijirewa wasiyyar Manzo na kin riko da littafin Allah da Iyalan gidansa masu tsarki a matsayin abin koyi da za su kaimu ga tsira duniya da lahira. To yanzu menene mafita?
Ya kamata al'umma su farka daga baccin da suke, su fahimci cewa basu da mafita ga siyasar Najeriya. Ya kamata su wayinci yaudarar da ake musu da cuta da sunan ceto, su karkato da hankulansu ga mai tausayinsu wanda kuma zai share hawayensu ya tseratar dasu daga kaskancin duniya dana lahira.
Kamar yadda nayi bayanin cewa, kaucewa wasiyyar Annabi na kin yin riko da Qur'ani da Iyalan gidansa shine ya saka mu a cikin wannan rayuwar ta kaskanci da muke ciki, kenan bamu da mafitar daya wuce mu dawo muyi riko da wannan wasiyya ta Annabi(s). To sai mu duba mu gani yanzu haka a fadin kasarnan waye yake kiran al'umma akan su dawo subi wannan tafarki na wasiyyar Annabi?
Bamu da wata amsa daya wuce muce Shaikh Ibraheem Zakzaky(h), domin kuwa kowa zaiyi shaidar cewa tun tasowarsa bashi da wani buri daya wuce ya fuskantar da al'umma hakikanin hanyar rabautarsu ta hanyar yin riko da wasiyyar Annabi(s)( Al'qur'ani da Iyalan gidansa).
Idanko haka ne, kenan babu wata dama data rage wa al'ummar Najeriya, illa yin riko ga Sayyeed Zakzaky da sallama masa, domin samun tsira anan duniya da kuma ranar lahira. Idan ko ba haka ba to lallai babu ranar karewar wannan rayuwar ta kaskanci da ake ciki, kuma kullum abin gaba zaita yi babu ranar samun sassauci, domin kuwa hanyar tsirar kwara daya ce Qur'ani da Ahlul bait(a.s) kuma kowa ya san cewa Sayyeed Zakzaky shi kadaine yake kira akan wannan hanya.
Don haka duk mai son tsira ya daina tunanin samun ceto daga wajan azzalumi, ya nemi ceto daga adilai. Don haka mudai mun fahimta kuma mun amsa kiran Jagoran da zai kaimu ga tsira anan duniya da lahira, kaima d'an uwa/'yar uwa zo ka/ki shiga jirgin kada ya d'aga babu kai/ke. LABBAIKA YAA AL-ZAKZAKY !!!
- Abbakar Ibraheem Kudan
21/02/2020
Tags:
Tunatarwa