@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Ya zo cikin hadisi daga Imam Ali(A.S )yana cewa:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ MAFI SHARRIN MUTANE SHINE WANDA YA KASANCE YANA BIBIYAR AIBOBIN MUTANE, KUMA MAKAHO GA AIBOBINSA .‘’
(Taraa'iful Hikaam, sh:176)
DARASI
Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, a kowanne lokaci mutum ya kasance mai duba gazawarsa wajen alaqarsa da Ubanginsa da kuma mu'amalarsa da jama'a, inda yaga ya gaza sai ya gyara don kyautata lahirarsa. Har ma ya zama abin koyi ga wasu.
Shi kuma hangen laifi ko gazawar wasu kan sa mutum ya riqa ganin laifinsu da zubewar darajarsu a gunsa . Sannan kuma wannan hangen nasa ba zai taba barinsa ya hangi tasa garawar ba ballantana ya gyara, zai tafi hakane a matsayin shine mai yin daidai .
Idan kuwa haka ta faru ga mutum yadda yake gani shi ba shi da laifi ko gazawa, to, ya yi hasarar duniya da lahira.
‘’ THE MOST VICIOUS PERSON IS HE WHO LOOKS FOR OTHER PEOPLE'S DEFECTS WHILE HE OVERLOOKS HIS OWN FAULTS .‘’
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~8th February, 2020.
Tags:
Tunatarwa