WHO| Abuja, Kano, Legas da jihohi 6 na cikin haɗarin ɓullar Coronavirus!!!


Ma'asuma Nigeria News Updates

Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Abuja, Kano, Legas, Cross River, Akwa Ibom, Port Harcourt, Enugu, Delta da Bayelsa matsayin jihohin da ya kamata a shirya matakan tsaro idan cutar Coronavirus ta bulla a Najeriya. Babbar jami'ar WHO, Dhamari Naidoo, ta bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata a taron horar da yan jarida kan cutar Coronavirus. Tace: "Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Najeriya matsayin kasa mai mugun hadarin kamuwa da cutar saboda yawan sufuri tsakanin kasar Sin da Najeriya." Ta ce WHO na aiki kan karfafa tsaro a iyakokin shiga Najeriya da kuma taimakawa wajen gano zafin jiki da fuskokin masu shigowa. Dhamari Naidoo ta kara da cewa an sanar da dukkan kamfanonin jiragen sama su yi kyakkyawan lura da masu shigowa Najeriya daga Sin. Abuja, Kano, Legas da jihohi 6 na cikin hadarin bullar Coronavirus - WHO Source: Depositphotos Mun kawo muku rahoton cewa kididdigan alkalumma sun tabbatar da cutar Corona Virus ta kashe sama da mutane 900 a kasar Sin, watau China tun bayan bullatar watanni biyu da suka gabata, inji rahoton gidan talabijin na Channels. Wadannan alkalumma sun tabbatar da cewa barnar da Corona Virus ta yi ya haura wanda cutar SARS ta yi a lokacin da ta zama annoba a tsakanin shekarar 2002 da 2003, koda yake dai kungiyar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta ce cutar da sauki yanzu. KU KARANTA: Badakalar N150bn: EFCC ta haramtawa tsohon gwamnan Abia da yaransa biyu fita daga Najeriya A shekarar 2002-2003 da cutar SARS ta barke, ta kashe mutane 774, amma biyo bayan samun karin mutane 91 da cutar Corona Virus ta kashe a lardin Hubei na kasar China a yan kwanakin nan, yasa Corona ta dara SARS wajen yin barna. Kungiyar WHO ta bayyana cewa a kwanaki hudu da suka gabata an samu dan saukin cutar a yankin Hubei, amma ta yi gargadin akwai yiwuwar kara samun mace mace a sakamakon yaduwar cutar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post