KU ZAMA MASU GIRMAN KAI !!!

 bai halasta ga mumini ya kaskantar da kansa (tawadi'u) ga kafirai da mushirikai ba.

@ma'asumah Nigerian news
Update, abbagano✍

Amman ya halasta ka kankantar da kanka (tawadi'u)  ga yan uwan ka muminai, domin Hakan yana daga cikin mafi girman ibadu.

Allah (t) yafadi hakan cikin kur'ani:-

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا مَن يَرْتَدَّ مِنكُمْ عَن دِينِهِ فَسَوْفَ يَأْتِي اللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوْمَةَ لَائِمٍ ۚ ذَٰلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ )

المائدة (54) Al-Maaida

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi.

MENE NE KASKAN DAKAI (TAWADI'U)

Tawadi'u shine kada ka irga kanka Wanda yafi wani.
Tawadi'u yana daga cikin kyautata halaye tare da mutane, hakan ne ma yasa Allah (t)  yasa shi cikin kebantattun ibadun sa. 

Kamar yadda yace :-

( وَعِبَادُ الرَّحْمَٰنِ الَّذِينَ يَمْشُونَ عَلَى الْأَرْضِ هَوْنًا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ الْجَاهِلُونَ قَالُوا سَلَامًا )

الفرقان (63) Al-Furqaan

Kuma bãyin Mai rahama su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya).

HADISAI KAN KASKANTAR GA KAI (TAWADI'U) 

Wanda yake tawadi'u saboda Allah, to Allah zai daga shi a idon mutane. 

(من تواضع لله رفعه الله فهو نفسه ضعيف وفي أعين الناس عظيم)
      —(كنز العمال:ج ٣ ب ٠٤ الرواية ٢

Tawadi'u ni'ima ce daba"a hassada akanta. 

(التواضع نعمة لا يحسد عليها)  

    —(الآداب الإسلامية ج_٧٨ ب ٢٩

KISSAR ANNABI ISAH KAN TAWADI'U

An rawaito cewa annabi isah yacewa mutanen sa, shin zaku bini? Nagaya muku?  Suka ce" zamu bika ya annabin Allah,se annabi isah ya mike tsaye yana wanke kafafun mutanen sa, daya bayan daya, duk dayake sunji wani iri, sede sunce zasu bishi, bazasu ce komi ba, 
Yayin daya gama, se sukace ya Malamin mu, mune yakamata mu wanke maka kafar ka, Amman se gashi kai katashi kana wanke tamu, se annabi isah yace :-  nayi haka ne dan nasanar daku, cewa mafi karamcin mutane,shine Wanda yake hidimtawautane, don haka yazama hanyar ku, tawadi'u. Domin tawadi'u yana komawa ga wanda yayi shi cikin aminci.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post