Kotu ta ɗaure matashin da ya yi wa Sheikh Zakzaky ɓatanci!!!


@Ma'asumah Nigerian News Update@

-Daga Shafin Yusuf Waliy


A ranar talata (4/2/2020) ne wata Kotun Majistiri da ke Potiskum, jihar Yobe ta daure wani matashi, daurin watanni shida a gidan yari ko tarar N10,000 bisa samunsa da laifin neman bata sunan Sheikh Zakzaky, a wani bidiyo da ya saki a dandalin sada zumunta na intanet.
     Asalin abin shi ne, a ranar litinin din da ta gabata 26/01/2020 ne, 'Yan 'uwa musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky, suka ci karo da wani bidiyo da ke yawo a intanet da dandalinsa na sada zumunta na cewa ana Gwanjon Mata a Potiskum.

Bidiyon na tsawon mintuna 2 da dakika 40,  a kusan karshensa sa aka sa hoton Jagoran harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky, mai dauke da rubutun 'Free Zakzaky.'
    Ganin bidiyon ya yi matukar daga hankali ga almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky, kasancewar yadda aka nuna hotunan mata ba hijabi, aka ci zarafinsu, karshe aka hada da hoton Sheikh Zakzaky.

   'Yan 'uwa sun ci gaba da bincike tun daga lokacin da suka yi arba da wannan bidiyon har zuwa ranar Litinin 3/2/2020, inda suka samu nasarar gamuwa da wanda ya yi wannan mummunan aiki a lokacin da ya ke kokarin sake fitar da wani sabon bidiyon a garin Potiskum.
    Ganin mai wannan aikin ke da wuya 'yan 'uwa suka kai shi kara gaban DPO na 'yan sandan Potiskum din, inda nan take ya bada umarni ga 'yan sandan da su tsare wanda ake zargi da aikata laifin.

 Bayan gudanar da bincike da 'yan sandan suka yi a ranar Litinin, ya kwana a hannunsu, washegari Talata 4/2/2020, sai suka gabatar da shi a gaban Kotun Majistiri da ke garin na Potiskum.
     Bayan karanta karar a gaban mai Shari'a Alagarno, da aka yi, ya tambayi wanda ake zargi,  Mohammad Garba, cewa; "Kaji abin da ake tuhumarka da shi?" Ya amsa da ya ji, kuma ya yarda ya aikata.

Sai mai Shari'ar ya sake tambayar sa cewa; "Me yasa ka aikata haka?" Cikin nadama ya ce; "Gafatta Malam na yi kuskure, kuma ina rokon kotu ta min afuwa cikin hukuncin da za'a yanke min."
    Duba da amsa laifin da kuma rokon da ya yi ga wanda suka shigar da kara da kuma Kotu, Alkalin ya yanke masa hukuncin Daurin wata shida a gidan Kaso ko tarar 10,000.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post