@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ALLAH YA KAWO MU CIKIN ZAMANIN
Irin wadannan kalmomi da Manzon Allah (S.A.W.W )ya riqa furta su ga sahabbansa sukan kasance tamkar wani abin al'ajabi a wancan zamanin.
Sai dai ga mu na wannan zamani bs ya zama abin mamaki, domin ya zo ne a daidai irin yanayin da al'ummar ke ciki.
Manzon Allah (S.A.W.W ) yana fadawa sahabbansa cewa ;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ DA SANNU ZAI ZOWA AL'UMMATA , SUNA SON ABUBUWA BIYAR (5)SUNA MANTAWA DA ABUBUWA BIYAR (5);
SUNA SON DUNIYA KUMA SUNA MANTAWA DA LAHIRA ,
SUNA SON DUKIYA KUMA SUNA MANTAWA DA HISABI,
SUNA SON MATA KUMA SUNA MANTAWA DA HURUL-EEN (matan aljannah ),
SUNA SON (ginin )BENAYE KUMA SUNA MANTAWA DA QABURBURA (graves ),
SUNA SON KANSU KUMA SUNA MANTAWA DA UBANGIJI .
TO, WADANNAN SUN BARRANTA DAGA GARE NI, NI MA NA BARRANTA DAGA GARE SU .‘’
(Ithnah Ashariyyah, shafi na 202).
Idan muka nazarci wannan hadisi da kyau za muga lalle duk wanda ya rungumi duniya da gaban qirjinsa, to, yakan manta da lahira . Kuma da ace mutum na tsoron hisabi to da ba zai so dukiya tazo masa ta ko'ina ba, sannan da ba zai sake matan duniya su rudar da shi ba matuqar yana tunanin na aljannah .
Sa'annan sai kaga a kullum mutane qasar qera gidaje suke yi ba tunanin aikata abinda zai haskaka musu qabarinsu ba, alhali shine gidan zamansu na qarshe. Kuma da ace a kowanne lokaci suna tunawa da Allah mahaliccinsu, to, da ba za su riqa biyewa son zuciyarsu ba, domin ita ta kasance mai umarni ce da munanan ayyuka .
ALLAH YA AMFANAR DAMU DAGA WANNAN TUNATARWA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~7th February, 2020.
Tags:
Tunatarwa