Ko kun san: Albarkar dake cikin cin abinci tare da jama'a!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KA CI ABINCI TARE DA WANI YA FI ALBARKA FIYE DA KACI KAI KADAI

Wani lokaci yanayi ne ke sa mutum yaci abinci shi kadai, wani kuma rowa ce ke sa shi yin haka, alhali Annabi (S.A.W.W )ya kwadaitar damu game da falalar cin abinci tare da wani. Yana cewa;

‘’ ABINCIN MUTUM 'DAYA YA ISHI MUTANE BIYU, ABINCIN MUTANE BIYU KUMA YA ISHI MUTANE UKU.....‘’

Sai dai mutane suna nisantar wannan al'amari mai falala.

Ku biyoni cikin wannan hadisi da ke biye;

Imam Ahmad ya riwaito ; Yazeed dan bawan ubanjigansa (ABDU-RABBIHI )ya bamu labari , Walid Bn Muslim ya bamu labari daga Wahshiy Bn Harb , daga babansa daga kakansa cewa;Wani mutum ya ce ga Annabi (S.A.W.W ),

‘’ Mu muna ci amma ba ma qoshi .‘’ Sai yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ WATAQILA KUNA CI A 'DAI-'DAI-KU NE (individual/separately ), KU HADU AKAN ABINCINKU (yayin ci ), KU AMBACI SUNAN ALLAH ZAI SANYA MUKU ALBARKA A CIKINSA .‘’

- Musnad Ahmad, J:3, SH:501.

Abu Dawud da Ibn Majah su ma sun riwaito, daga hadisin Walid Bn Muslim.

- Sunan Abu Dawud, J:3, SH:346.

- Sunan Ibn Majah, J:2, SH:1093.

Don neman albarka muka kawo wannan riwaya, amma babu laifi in kun ci ku kadai bisa wata lalura ta kadaitaka ko wani yanayi, amma ba bisa rowa ba.

Allah (T )na cewa;

‘’ ....BABU LAIFI A KANKU DA KU CI GABA 'DAYA (cikin jam'i )KO DABAN-DAB...‘’

(Suratul-Nurr, aya ta 61).

Wannan dalili kuwa an kawo shi ne don talakawa wadanda ba su da wadatar cin mai kyau ko shan mai kyau. Domin idan kana ci ko kina ci tare da masu watada wataqila su riqa raina muku abincinku, saboda haka sai kowa yaci nasa shi kadai don mutunta kai.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

07059911360-09039791509

~20th February, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post