Yaune Yan'uwa Mata na Kano da kewaye suka gabatar da Khatamar Mauludin Sayyida Zahara (as) a Markazin Yan'uwa na Kano dake Kofar waika.
Taron Ya Sami Al'barkar Zuwan Uwar Gidan Sheik Turi Malama Maimunatu Abdullahi.
Malama Jamila Auwwal Uwar Gidan Sheik Muktar Sahabi daga Kaduna itace Babbar Bakuwa mai Jawabi,
Haka taron ya sami halartar Malaman Wahada Mata irinsu Shugabar Mata ta Darikar Kadiriya ta Africa Malama Baraka daga Darul Kadiriya, da sauran Malam Wahada.
Cikin Jawabinta Malama Jamila ta Jawo hankalin Yan'uwa mata da sukula da Hijabi sukuma bashi Mahimmanci ganin yadda suke sakaci dashi a wani lokacin.
Haka kuma tayi kira ga Yan'uwa Maza da su sauke nauyin Yan'uwa mata da Allah ya dora musu daidai Gwargwado.
da take Ta'aliki ga Malama Jamila, Malama maimunatu Abdullagi Uwar Gidan Sheik Turi,
tafara da gaishe da Yan'uwa ganin Tsawan Wata Goma ba'ahadu da Junaba, tace anan ba Muhallin yin bayanin Dalilan hakan bane, kuma ba zata tsawaita da bayani ba.
abinda zatayi kira ga Yan'uwa shine komai zasuyi suyi dan Allah.
Bayan gama Jawabai an bada dama ga Yan'uwa Maza su taso su bayyana Kyatukansu na Karramawa ga Matansu Kamar yadda Su Maulanmu Sheik Ibraheem Zakzaky (h) sukayi nuni dayin hakan a irin wannan Rana.
Yan'uwa sunrika tasowa suna Al'kawarin Dubban Nairori, wasuma suna badawa awajan, haka kuma wasu sun bada Manyan kyauka irinsu Motoci, da Kojirun Umara, harda na Ziyarar Karbala.
Cikin kaytukan da sukaja Hankali akwai wadda Injinya Yahaya Gilima Kaduna ya gabatar ga Iyalansa na kyautar Dubu Dari Dari, saikuma Dubu Talatin ga Iyalan Shahidai Mata.
Sai kuma kyautar da Shahararran Mawakin Imamu Hussain (as) da Malam Zakzaky(h) yayi Wato Zaharadden Kode, inda ya bada kyautar Kujarar Zuwa Karbala ga Matansa Uku rigis tare da biyawa Mahaifiyarsa kujerar Umara.
Bikin Khatamar Mauludin ya kayatar matuka yayinda ,zukatan Mahalartansa suka cika da Farinciki.
daga karshe anbada kyautaka ga Malaman Wahada, dakuma Halkoki, da Yankunan da sukayi na daya zuwa na Uku.
Akasa Wasu daga Hotunan da muka dauko muku ne.

Tags:
Munasabobi