@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ANNABI (S.A.W.W )YA YI HANI KAN HAKA.
Kashe rai ba bisa haqqi ba mummunan aiki ne wanda Allah (T ) ke qyamatarsa.
Ba ya halatta ka kashe rai bisa zalunci, kuma ko da bisa shari'a ce ba kowa ne ke da alhakin zartar da hukuncin ko aiwatar da shi ba.
Sannan a dokar yaqi ma na kafirai haramun ne a kashe mata da yara a yaqi matuqar ba makami suka dauka ba. Wannan yaqi kuwa na muslimci ne ko ba na muslimci ba.
Ibn Umar ya bada labarin abinda ya ji Annabi (S.A.W.W )ya fada dangane da abinda ya gani ya auki kan wata mata cikin wani yaqi.
Yake cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ LALLE MANZON ALLAH (S.A.W.W )YA GA WATA MATA A MACE (an kashe ta )CIKIN WANI YAQI, SAI YA QYAMACI HAKAN, KUMA YAYI HANI KAN KASHE MATA DA YARA .‘’
(Muwadda-Malik, hadisi me lamba: 965 ).
Amma shi Buhari ya sabawa dukkan wasu dokoki na muslimci dana dimokradiya, domin shi yakan kashe kowa-da-kowa, mata da yara, ba ma a halin yaqi ba sai dai don zalunci .
Ni har na rasa ma sunan da zan iya ba shi bisa dalilai kamar haka;
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
(1)- A muslimci haramun ne kashe rai haka siddan.
(2)- Addinin kiristanci ma sun barranta daga kashe rayuka.
(3)- Shi kuma Fir'auna ya yarda da kisan rayukan mazaje , amma banda rayukam mata.
To, shi kuma wannan dan ta'addan wanne suna,ne,ya fi dacewa da shi bisa tunaninku?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~18th February, 2020.
Tags:
Tunatarwa