A cikin Majma'ul Bayan, an kawo
ruwaya da isnadi daga Imam Ja'afarus Sadiq daga iyayensa daga Annabi (S)
yace:
"Yayin da Allah Mai girma da daukaka
ya saukar da wadannan ayoyi;
1- Fatiha
2- Ayatul Kursiyyu
3- Shahidallahu annahu La'ilaha illa
hawa wal Mala'ika...
4- Qulil lahumma Malikal Mulki...
(zuwa- Bigairi Hisab).
Sai wadannan ayoyin suka je suka
damfaru da Al'arshi, ba su da
shamaki tsakaninsu da Allah. Sai
suka ce; "Ya Rabbi, yanzu za ka
saukar da mu a gidan zunubai i zuwa
kuma ga halittun da suke saba maka,
alhali kuma mu muna manne da
Tsarki (Duhur da Qudus)?
Sai Allah (T) yace:
"Na rantse da
Izzata da buwayata duk wani Bawa
da karanta ku a karshen kowace
sallarsa, sai na tsugunar da shi a
tsattsakin Tsarki bisa abin da yake
kai (na aikinsa),
kuma na dube shi
da Idanuna tabbatattu kowace rana
Sau saba'in. Kuma kowace rana sai
na biya masa bukata 70, mafi
karancin bukatar shine yafe masa
(Zunubansa) kuma sai na kiyaye shi
daga kowane makiyi na dora shi
birbishin makiyin. Kuma ba abin da
zai hana shi shiga Aljanna sai
Mutuwa."
- Cikin Tafsirin Alkur'ani mai girma na
Sayyid Zakzaky. A karkashin Tafsirin
Suratul Fatiha.
Auwal Yusuf Muhammad
Ma'asumah Najeria news Updet
#9/2/2020
Tags:
Makaranta