@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MUMINI ABIN KWATANCE GA MUMINAI
Abu ne wanda in ka fade shi babu shakku ko batun cewa ba haka bane, sai dai kawai ayi jayayya ko kawar da kai don rashin jin tsoron Allah.
Shi kamanni ana yinsa ta yanayin qirar jiki ko launin fata, sannan kuma ana yinsa ta hanyar dabi'u ko halayya .
Kamanceceniyar da muke son kawowa anan ba ta fuskar halittar gangan jiki bane, sai dai a dabi'a da kuma irin yanayin da suka sami kansu ciki.
GA SU NAN KAMAR HAKA:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
(1)- HALAYYAR YABO A HALIN QURUCIYA:- Tun tasowar Sayyid (H )ta quruciya ba a taba samunsa da aikata wasu halayya na zargi ba.(2)- GASKIYA DA RIQON AMANA:- Ba a taba samun Sayyid Zazkzaky (H )yayi qarya cikin zantukansa (his normal speech )ko cin amanar wani ba.
(3)- CUTARWA/QIYAYYA DAGA WASU DANGINSA:- Yadda aka sami wasu daga cikin dangin Manzon Allah (S.A.W.W )da suka cutar da shi ta hanyar batanci ko qulla masa makirci, haka ma Sayyid (H )ba tare da laifin sa ba.
(4)- RASHIN CANZA MAGANA:- Tunda Sayyid (H )ya fara da'awarsa bai taba yin wata magana wacce daga baya ya canzata don ganin ya yi kuskure ba.
(5)- SAMUN MABIYA TSAYAYYU :- Shine kadai ke da mabiya wadanda cutarwar masu cutarwa bai sa su sun canza ba .
(6)- CUTARWAR MAQIYA AZZALUMAI :- Irin nau'in cutarwar da aka yiwa Manzon Allah (S.A.W.W )irinta ake yi masa da mabiyansa.
(7)- TAIMAKO DAGA ALLAH:- Irin taimakon da Annabi (S.A.W.W )ya samu daga Allah irinsa ne Sayyid Zakzaky (H )ke samu.
WADANNAN SUNE KADAN DAGA CIKI.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~15th February, 2020.