Jawabin Sheik Yaqub Yahaya a wajen Mauludin Sayyida Fatima na Zone (c) yayi tsokaci dangane da hakkin Shuhada

Bayan bude taro da Addu'a da karatun Alqur'ani da Raira baituka ga Sayyida Fatima zuwan Sheik Yaqub kenan ya hau Munbari sai ya fara tsokaci akan Hakkin Iyalan Shahidai.

Sheik Yaqub yace ( bazan kara ziyartar wata Halka ko inziyarci wani taro koda na Maulud ne duk wanda ya kara gayyatata wani taro koda ya gayyaceni bazance ba, domin rishin sauke hakkin Shuhada koda wani gari ne ba zanje ba!, idan har naje sai anbani Sunaye akan cewa anbiya wadannan Hakkin Shahidan sannan inje idan ba'a biya ba bazanjeba ko ina ne).

Dukkan wadan da keso inje taronsu ko gayyatarsu basu biya Kudin Hakin Shahidai ba! Suzo muzauna ayi sulhu da yarje-je niya sai inzo inba haka ba kada wanda ya kara gayyatata.

Bai kamata ace wasu mutane masu amsa sunansu na musilmai suna Sallah da karatun Alqur'ani ace suna gaba da jikokin Manzon Allah ba!, Ali, Fatima,  Hassan, Hussaini, ko yace bayason 'yan shi'a wannan babban kuskure ne, idan bakaso masoya Annabi da Iyalansa ba wa nene abin so a wajenka....?.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post