Iran: Ana Gudanar Da Bukukuwan Cikar Shekaru 41 Da Juyin Juya Hali

Tun da safiyar yau ne miliyoyin jama’a suka yi cincirindo a kan tituna dukkanin birananen kasar Iran, domin bukukuwan cikar shekaru 41 da juyin juya hali na kasar.

An gudanar da jerin gwano mafi girma a birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran a yau, tare da halartar manyan jami’an gwamnatin kasar, kamar yadda kuma miliyoyin jama’a suka halarta, inda aka gabatar da jawabai a dandalin ‘yanci da ke tsakiyar birnin.

Shugaban kasar ne Rauhani ne ya gabatar da jawabi, a gaban dimbin jama’a, inda ya jaddada cewa kasar tana nan daram kan bakanta na kin mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin mallaka.
Kafofin yada labarai da daman a ciki da wajen kasar sun bayar da rahotanni kai tsayea okacin gudanar da gangamin, inda tashar Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, a wannan karo tutocin kasar Iran da hotunan Kasim Sulaimani ne aka yi ta dagawa a wurin gangamin.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

Haka nan kuma kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da cikakken rahoto a kan tarukan da aka gudanar a kasar ta Iran a yau a birnin Tehran da sauran biranan kasar.


Kamar yadda kamfanin dillancin abaran Associated press ma ya bayar da rahoton da ke taron na yau yana daga cikin manyan taruka da aka taba yi kasar.


Baya ga haka ‘yan rahoto daga tashohin yada labarai da daman a duniya da suka halarci taron na yau, sun bayar da rahotanni masu kama da juna kan fitowar miliyoyin al’umma domin tunawa da ranar ta cikar juyin juya hali shekaru arba’in da daya a kasa


      ~Daga Ishaq Mohd Kibiya
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post