@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RABON GADO A MUSLIMCI .
Shi rabon gado umarni ne na Allah (T )wanda yayi umarnin aikata shi cikin makusantan mamaci.
Saboda girmansa dakuma hadarin da ke cikinsa yasa Allah ya raba shi da kansa (S.W.A )don gudun kada ma wani yazo yana cewa ba haka ya kamata ya kasance ba.
Raba abinda mamaci ya bari na gado ga magadansa shine mafi tsarki kuma mafi kwanciyar hankali ga magana. Rashin yinsa kan zama wata musifa tsakanin magada matuqar aka yi jinkirinsa, wani lokaci kuma yakan zama an zalunci wasu ko wani daga cikin magadan.
Shi kuma wannan ya zo ne cikin Qur'ani bisa jadawalin qasaru (fraction ), saboda haka haqiqanin sanin yadda za a raba shi dole sai da ilimin lissafi .
GA DAI YADDA YAZO A TSARIN QASARU .
1 1 1 1 2 1--- --- --- --- --- ---
2 4 8 3 3 6
(1)- 1
---
2,
Rabi, shine kason miji (husband ), 'ya guda 1, 'yar da (son's daughter ), cikakkiyar 'yar'uwa wacce ake ciki daya ko uba daya. Suna samun wannan kaso ne bisa wasu yanayi.
(2)- 1
---
4,
Kwata, shi kuma kaso ne na mata (wife )da miji,(husband ) bisa wani yanayi.
(3) 1
---
8,
'Daya bisa takwas, shine kason mata (wife )ko mata (wives ). Shima hakan kan faru ne bisa wani yanayi.
(4)- 1
---
3,
'Daya bisa uku, shine kason uwa (mother ), kason biyu ko sama da haka na 'yan'uwan da uwa ta hada (maza da mata ).
(5)- 2
---
3,
Biyu bisa uku, shine kason 'ya'ya mata biyu ko fiye da haka (na mamaci ), ko 'ya'ya mata biyu ko fiye da haka na 'ya'yan danka (your son's daugthers ), 'yan'uwa mata shaqiqai (full sisters ), da kuma 'yan'uwa mata biyu ko fiye da haka wadanda uba ya hada ku (your consanguine sisters ).
(6)- 1
---
6,
'Daya bisa shida, shine kason Uba, Uwa, kaka (namiji ), 'yar da(son's daughter )yayin da tayi gado da 'ya, 'yar'uwa li'abiya (consanguine sister )yayin da tayi gado tare da 'yar'uwa shaqiqiya .
ABIN LURA
―――――――
Shi magaji yakan ci kaso ne gwargwadon yadda ya sami kansa, domin samuwar wani daga cikin magada kan iya canza mutum daga wani matsayi zuwa kan wani matsayin .
A can baya mun taba yin rubutu mabambanta game da yadda ake yin rabon gado, amma bisa la'akari da yanayin da wasu ke shiga yasa muka qara yin waiwaye kan wannan babban al'amari mai sarqaqiya.
Za mu cigaba insha Allah.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~12th February, 2020.
Tags:
Taskar ilimi