@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AKWAI GYARA CIKIN WASU MATASAN NAMU.
A'imma (A.S )sun kasance mafiya sani (ilimi )akan sauran halittun Allah (T ), sannan sun kasance masu yin umarni game da neman ilimi.
'Daliban Ahlul-Bait (A.S )kuma su suka fi sauran daliban kowa ilimi ta kowanne fanni. Wannan dalili yasa ake samun tacaccen ilimi a wajen su.
Ganin irin tarbiyyah da ilimantarwar da A'imma (A.S )suke zazzagewa almajiransu yasa ba sa ganin za a iya samun wani jahili marar karatu daga cikin daliban su.
Har ma Imam Ja'afarus-Sadiq (A.S )ke cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ DA DAI ZA AZO DA WANI MATASHI DAGA MATASAN SHI'ARMU (mabiyanmu )KUMA BA YA NEMAN ILIMI, DA ZAI NA LADABTAR DA SHI !‘’
(Biharul-Anwar, J:1, SH:214)
Ni da naci karo da wannan hadisi kuma na kalli wasu matasa masu riya cewa su mabiyan Ahlul-Bait (A.S )sai abin ya bani tsoro.
Dalili kuwa shine, da yawa daga cikin su suna da aqidar cewa matuqar sun miqa wilayarsu ga Ahlul-Bait (A.S )sun sami wani lasisi (certificate )da zai kai su zuwa Aljannah ko da kuwa ba sa neman ilimi, kuma da kuwa sunyi watsi da wasu ayyukan wajiban da suka hau kansu.
To, a gaskiya masu irin wannan aqida sun saba koyarwar Ahlul-Bait (A.S ), sannan kuma sunyi hannun riga da mabiya 'yan shi'ar gaskiya , ko da kuwa suna tarayya da su cikin wasu ayyuka (programmes ).
A kullum jagoranmu Sayyid Zakzaky (H )kira yake mana da mu tashi kan neman ilimi da kuma aiki da shi . Kenan duk wanda ba ya neman ilimi ba zai zama abin alfahari wajen jagora ba, ballantana ga A'imma (A.S ).
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~9th February, 2020.
Tags:
Taskar ilimi