@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
WANI AIKI SAI QOFAR ILIMIN MANZON ALLAH (S.A.W.W ).
Ku nazarci wadannan riwayoyi biyu na bayin Allah salihai .
ANNABISULAIMAN(A.S )
Bukhari yace, Abu Yamani ya bamu labari, Shu'aibu ya bamu labari yace, Abu Zinad ya bamu labari daga Abdurrahman, daga Abu Huraira cewa, Manzon Allah (S .A.W.W )yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
‘’ WASU MATA BIYU SUNA DA 'YA'YANSU, SAI KERKECI (Zi'ibu )YAZO YA TAFI DA 'DAYANSU. SAI 'DAYAR TA CEWA 'YAR'UWARTA, KERKECI YA TAFI DA 'DANKI. SAI 'DAYAR MA TACE, ‘’ A'A, DA 'DANKI YA TAFI .‘’ SAI SUKA TAFI WAJEN DAUDA (A.S )DON YAYI MUSU HUKUNCI. SAI YA BAIWA BABBAR WANNAN YARO . SAI SUKA FITO WAJEN SULAIMAN 'DAN DAWUD (A.S )SUKA BA SHI LABARI . SAI YACE;
‘’ KU ZO MIN DA WUQA NA RABA MUSU SHI GIDA BIYU . SAI QARAMAR TACE; ‘’ Kada ka aikata, Allah yayi ma rahma, danta ne .‘’
SAI AKAYI HUKUNCI TA HANYAR BAWA QARAMAR (saboda an tabbatar danta ne ta hanyar yadda uwa ke so da tausayin danta ).
Abu Huraira yace, ‘’ Wallahi ban taba jin hukunci da wuqa ba sai wannan lokaci .‘
’
(BUKHARI , HADISI MAI LAMBA 6769)
IMAM ALI (A.S)
Wani hukunci ne ya gagari Sahabbai warwarewa sai aka kai shi ga Umar Bn Khaddab (mai rarrabe qarya da gaskiya )don ya warware musu. Sai Umar yace;
‘’ AI WANNAN HUKUNCI SAI 'DAN ABU 'DALIB !‘’
Sai jama'a suka ce ai kaine mai yankewa da zartarwa. Jayayya tayi yawa sai ya tilasta su zuwa wajen Imam Ali (A.S ). Sai Umar yace masa;
‘’ WANI MUTUM NE KE DA MATA BIYU MASU CIKI, TO, SAI SUKA HAIHU CIKIN DARE 'DAYA. 'DAYA MACE 'DAYA NAMIJI. TO, SAI RIGIMA TA KAURE TSAKANINSU, KOWACCE TACE NATA NE NAMIJI DON KWADAYIN GADO.‘’
Sai Ali ya dauki wani abu daga,qasa ya daga sama yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ ('Daga )WANNAN SHI YAFI WAHALA DAGA WANNAN HUKUNCI !‘’
Sai Imam Ali (A.S )yace kowacce ta tatso nononta (na shayarwa ), aka zuba a mazubi dabandabam . Sai aka auna nawin nonon nasu, sai aka sami na dayarsu rabin nawin na 'yar'uwarta ne. Sai aka bada da namiji ga wacce nononta yafi nawi.
Imam Ali (A.S )yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ NONON (shayarwa na )MACE RABI NE AKAN NONON NAMIJI KAMAR YADDA GADONSU YAKE .‘’
Umar yayi mamaki, sannan yace;
‘’ YAA BABAN HASSAN, KADA ALLAH YA BARNI CIKIN WANI TSANANI WANDA BA KA NAN (a wajen )!‘’
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~20th February, 2020.
Tags:
Taskar ilimi