@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SIFFAR JAGORANA SAYYID ZAKZAKY (H )KENAN.
A wannan zamani da muke ciki an fi ganin daraja ko girman masu dukiya ko mulki da sarauta . Duk wani abinda za ka mallaka matuqar ba wadannan bane, to, kai ba komai bane a duniyanci.
Sai dai abin ba haka yake a wajen Allah da Manzonsa (S.S.W.W ), domin a wajen matuqar kana da wadannan abubuwa tare da kai, to, babu abinda ya kubuce maka a duniya da lahira .
Karanta ka gani, shin, wanda kake bi a duniyance ko a addinance na da wadannan (qualities )?
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Imam Ahmad Bn Hambal yace, Hassan ya bamu labari, Ibn Lu'ata ya bamu labari daga Harith Bn Yazid Al-Hadhramiy , daga Abdullahi Bn Amru cewa;Manzon Allah (S.A.W.W ) yace;
‘’ ABUBUWA HUDU (4)IDAM YA KASANCE KANA DASU TO, BABU ABINDA YA KUBUCE MAKA DAGA DUNIYA;
-TSARE AMANA;
-GASKIYAR MAGANA;
-KYAWAWAN 'DABI'U; da
-QARANTA (cin )ABINCI .‘’
(Musnad Ahmad J:2, SH:177).
Wadannan siffofi ana samun su ne kadai wajen mumini, shi kuma mumini babu abinda ke kubuce masa na alheri duniya da lahira.
Idan ka kalli wannan hadisi kuma ka kalli Sayyid Zakzaky (H )sai kace hadisin ma na magana ne a kansa.
☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾
PLS, KA QARA KARANTA HADISIN SOSAI, SANNAN KA AUNA SHI DA 'DABI'UN MALAMANKA !
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034-09039791509
~9th February, 2020.
Tags:
Jagoran Gaskiya