Ibn Taimiyyya, jagoran zagin sahabbai da ƙaryata hadisan Manzon Allah (S)!!!


MA'ASUMAH NIGERIAN
NEWS UPDATE

M.N.U.030

AZ-ZAHABI, AL-BANI...
SUN TABBTAR DA; IBN
TAIMIYYA BA SHI DA
AMANAR ILIMI; SBODA
IBN TAIMIYYA YA KAN
KARYATA HADISAN DA
MALAMAN HADISI
SUKA TABBATAR DA
INGANCINSU. SANNAN
YA INGANTA HADISAN
DA MALAMAN HADISI
SUKA TABBATAR DA
RAUNINSU:
 ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺗﻌﻠﻴﻘﺎ ﻋﻠﻰ ﺣﺪﻳﺚ(
ﻣﺎ ﺗﺮﻳﺪﻭﻥ ﻣﻦ ﻋﻠﻲ؟ ﺇﻥ ﻋﻠﻴﺎ
ﻣﻨﻲ ﻭﺃﻧﺎ ﻣﻨﻪ ﻭﻫﻮ ﻭﻟﻲ ﻛﻞ ﻣﺆﻣﻦ
ﺑﻌﺪﻱ ( ﻛﻤﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ
 ، ﺣﺪﻳﺚ263 / 5ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ 
2223 :
Sanannan malamin
hadisi a wajen
Salafawa, kuma dan
gani-kashenin
Wahabiyanci;
Nasurudden Al-bani. Ya
tabbatar mana cewa;
tabbas Ibn Taimiyya
yana da son rai wajen
inganta hadisai da
raunatasu. Lokacin da
Al-bani yake ta'aliki akan
hadisi ingantacce kuma
mutawaturi da Ibn
Taimiyya ya karyata,
wanda Annabi
Muhammad(saw) ya ke
cewa:
"...Ali(as) daga gareni
yake, nima daga gare
shi nake (duk abinda
Imam Ali(as) yayi
tamkar Annabi(saw) ne
yayi), kuma shine
shugaban kowane
mumini a bayana..."
Sai Al-bani yace;
ﻓﻤﻦ ﺍﻟﻌﺠﻴﺐ ﺣﻘﺎ ﺃﻥ ﻳﺘﺠﺮﺃ ﺷﻴﺦ
ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﻋﻠﻰ ﺇﻧﻜﺎﺭ ﻫﺬﺍ
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭﺗﻜﺬﻳﺒﻪ ﻓﻲ " ﻣﻨﻬﺎﺝ
 ( ﻛﻤﺎ ﻓﻌﻞ104 / 4ﺍﻟﺴﻨﺔ " ) 
ﺑﺎﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻤﺘﻘﺪﻡ ﻫﻨﺎﻙ ..... ﻓﻼ
ﺃﺩﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻭﺟﻪ ﺗﻜﺬﻳﺒﻪ
ﻟﻠﺤﺪﻳﺚ ﺇﻻ ﺍﻟﺘﺴﺮﻉ ﻭﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﺮﺩ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ، ﻏﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻨﺎ
ﻭﻟﻪ ( ﺃﻫـ
"Abin mamaki ne sosai,
a ce; Ibn Taimiyya ya
runtse ido ya yi inkarin
(ingancin) wannan
hadisi, har ma ta kai ga
ya karyata wannan
hadisin, a Minhajus-
Sunnah, juzi'i na 4,
shafina 104, kamar
yanda (Ibn Taimiyya) ya
karyata hadisin da ya
gabace shi (wanda
Annabi(saw) yake cewa:
"Duk wanda na kasance
shugabansa to Ali(as)
ma shugabansa ne"). (Al
-bani ya ce) ban san
dalilin da zai sa Ibn
Taimiyya ya karyata
wannan hadisi ba, face
gaggawa (rashin
natsuwa ta ilimi) da
wuce gona-da-iri wajen
yiwa 'yan Shia raddi,
Allah ya gafarta mana
da shi (Ibn Taimiyya)".
(Silsilatul-Ahadisus-
Sahiha, juzi'i na 5,
shafina 263, hadisi na
2223).
Cewar da Al-bani yayi:
ﻓﻼ ﺃﺩﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻭﺟﻪ ﺗﻜﺬﻳﺒﻪ
ﻟﻠﺤﺪﻳﺚ ﺇﻻ ﺍﻟﺘﺴﺮﻉ ﻭﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ
(ban san dalilin da zai
sa Ibn Taimiyya ya
karyata wannan hadisi
ba, face gaggawa
(rashin natsuwa ta ilimi)
da wuce gona da iri...).
Hakan yana tabbatar
mana da cewa; Ibn
Taimiyya ko dai jahilin
ilmin Hadisi ne ko kuma
mai tsaninin son rai
akan Hadisai. Idan ba
haka ba, ba abinda zai
sa Ibn Taimiyya ya
runtse ido ya karyata
mutawaturin hadisi.
Kuma abinda ya bawa
Al-bani mamaki shine;
Ibn Taimiyya ya karyata
hadisin ba tare da ya
kawo hujja daga ilimin
hadisi ba. Kamar dai Ibn
Taimiyya yana so ya ce;
Annabi(saw) ne ya bashi
damar ya karyata
hadisin da ya ga dama
ya kuma inganta wanda
ya ga dama.
Al-bani ya tabbatar da
Ibn Taimiyya yayi
babban zunubi ta hanyar
karyata ingantaccen
hadisi, shiyasa Al-bani
ya ce; ﻏﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻨﺎ ﻭﻟﻪ (Allah
ya gafarta mana da shi
(Ibn Taimiyya). Kenan Al
-bani ya tabbatar mana
rashin amanar ilimi ga
Ibn Taimiyya. Da Ibn
Taimiyya yana da
amana ta ilimi da ba zai
karyata hadisi
ingantacce ba.
ﻭ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻲ ﻻ ﻳﻌﻮﻝ ﻋﻠﻰ ﺗﺼﺤﻴﺢ
ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﻭﻻ ﻋﻠﻰ ﺗﻀﻌﻴﻔﻪ
ﻟﻼﺣﺎﺩﻳﺚ ﺑﻞ ﻳﻨﺼﺢ ﻃﻼﺏ
ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻥ ﻻ ﻳﻌﻮﻟﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻳﻀﺎ
Wani abinda ya kamata
mu lura da shi anan
shine, tamkar Al-bani ya
fito karara yana nunawa
daliban ilimi cewa; kar
su dogara da ingantawa
ko raunatawar Ibn
Taimiyya ga hadisai,
don yana da son zuciya.
Al-bani ya nuna karara,
shi kansa da yake
dalibin Ibn Taimiyya
amma yafi Ibn Taimiyya
sanin hadisai ingantattu.
Wannan yasa Al-bani ya
rubuta littafin ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﻜﻠﻢ
ﺍﻟﻄﻴﺐ don fitar da
hadisai marasa inganci
daga littafin Ibn
Taimiyya mai suna ﺍﻟﻜﻠﻢ
ﺍﻟﻄﻴﺐ .
ﻭﻳﺆﻛﺪ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻲ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺫﻟﻚ ﻭﻣﻦ
ﺍﻣﺜﻠﺘﻪ : ﻗﻮﻟﻪ ﻓﻲ ) ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﻜﻠﻢ
4 : ﺍﻟﻄﻴﺐ ( ﻻﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ) ﺻﺤﻴﻔﺔ
 ﻩ ( ﻣﺎ1400ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻟﺮﺍﺑﻌﺔ (
ﻧﺼﻪ :
Ga abinda Al-bani yake
cewa akan littafin Ibn
Taimiyya mai suna ﺍﻟﻜﻠﻢ
ﺍﻟﻄﻴﺐ :
ﺍﻧﺼﺢ ﻟﻜﻞ ﻣﻦ ﻭﻗﻒ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺃﻭ ﻏﻴﺮﻩ ﺃﻥ ﻻ ﻳﺒﺎﺩﺭ ﺍﻟﻰ
ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﻤﺎ ﻓﻴﻪ ﻣﻦ ﺍﻻﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻻ
ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺘﺎﻛﺪ ﻣﻦ ﺛﺒﻮﺗﻬﺎ، ﻭﻗﺪ ﺳﻬﻠﻨﺎ
ﻟﻪ ﺍﻟﺴﺒﻴﻞ ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﻋﻠﻘﻨﺎﻩ
ﻋﻠﻴﻬﺎ، ﻓﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﺛﺎﺑﺘﺎ ﻣﻨﻬﺎ ﻋﻤﻞ ﺑﻪ
ﻭﻋﺾ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﻨﻮﺍﺟﺬ ﻭﺍﻻ ﻓﺎﺗﺮﻛﻪ ..
. ﺍﻧﺘﻬﻰ ﻓﺘﺄﻣﻞ ( !
"Duk wanda zai karanta
wannan littafin (na Ibn
Taimiyya) ko wanin
wannan littafin (daga
littafan Ibn Taimiyya) to
kar yayi saurin aiki da
hadisan da ke ciki, har
sai ya tabbatar da
ingancinsu, kuma mun
sharewa (mai karatun
littattafan Ibn Taimiyya)
hanya, ta hanyar rubuta (
ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﻜﻠﻢ ﺍﻟﻄﻴﺐ ), abinda
muka tabbatar da
ingancinsa a littafin to
za'a iya riko da shi,
abinda muka tabbatar
da rashin ingancinsa sai
ayi watsi da shi (a
barwa Ibn Taimiyya
kayansa)".
ﻓﺎﻻﻟﺒﺎﻧﻲ ﻳﻘﻮﻝ ﺑﺼﺮﺍﺣﺔ : ﺍﺭﺟﻌﻮﺍ
ﻟﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭﻻ ﺗﺮﺟﻌﻮﺍ ﺍﻟﻰ
ﺷﻴﺦ ﺍﻻﺳﻼﻡ ! ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ! ﻓﻴﺎ
ﻟﻠﻌﺠﺐ ! ﻓﻌﻠﻰ ﻣﻦ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﺍﻥ
ﻳﻌﻮﻝ ﻃﻼﺏ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻋﻠﻰ
ﺗﺼﺤﻴﺤﺎﺕ ﻭﺗﻀﻌﻴﻔﺎﺕ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ
ﺍﻡ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻲ؟
Kenan Al-bani ya
tabbatar mana yafi
malaminsa a akida
ilimin sanin hadisi?
Kenan Ibn Taimiyya ba
abin dogaro bane wajen
ingantawa ko raunata
hadisai? Tamkar dai Al-
bani yana so yace; yafi
Ibn Taimiyya zama abin
dogaro a ilimin hadisi?
ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻳﺼﻒ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺑﺎﻧﻪ
ﺟﺮﺉ ﻋﻠﻰ ﺗﻜﺬﻳﺐ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ
ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ .
Kamar yanda dai Al-bani
ya fada; Ibn Taimiyya ya
na da gaggawa (rashin
natsuwa ta ilimi) da
wuce gona da iri wajen
karyata hadisai
ingantattu.
Kalli yanda Ibn Taimiyya
ya karyata hadisul-
Ghadir, har yake da'awar
hadisin bai zo a
littattafai ingantattu ba,
wai wasu malamai (yan
kadan) ne suka riwaito
shi, wai ma akwai
sabani ma akan
ingancin hadisin.
 ﺍﻭﺭﺩ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺣﺪﻳﺜﺎ ﻓﻲ(
 ( ﻓﻴﻪ86 / 4ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺳﻨﺘﻪ ( ) 
ﻓﻀﻞ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ
) ﻉ ( ﻓﺎﺩﻋﻰ ﺑﺎﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﺼﺢ
ﺍﻋﺘﻤﺎﺩﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﺑﻦ ﺣﺰﻡ ﺣﻴﺚ ﻗﺎﻝ
ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ : ] ﻭﺍﻣﺎ ﻗﻮﻟﻪ : ) ﻣﻦ
ﻛﻨﺖ ﻣﻮﻻﻩ ﻓﻌﻠﻲ ﻣﻮﻻﻩ ( ﻓﻠﻴﺲ
ﻫﻮ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﺎﺡ، ﻟﻜﻦ ﻫﻮ ﻣﻤﺎ
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎء، ﻭﺗﻨﺎﺯﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ
ﺻﺤﺘﻪ ... [ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ ﻧﻘﻼ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ
ﺣﺰﻡ ﺑﺰﻋﻤﻪ : ] ﻗﺎﻝ : ﻭﺍﻣﺎ ) ﻣﻦ
ﻛﻨﺖ ﻣﻮﻻﻩ ﻓﻌﻠﻲ ﻣﻮﻻﻩ ( ﻓﻼ
 ﻳﺼﺢ ﻣﻦ ﻃﺮﻳﻖ ﺍﻟﺜﻘﺎﺕ ﺍﺻﻼ] .
ﺍﻩ
Sai kuma gashi
dalibinsa a akida;
Shamsuddeen Az-
Zahabi yana karyata Ibn
Taimiyya da cewa
hadisin Ghadir
mutawaturi ne da ba
shakka akan ingancinsa,
Az-Zahabi ya tabbatar
da haka a littafinsa;
Siyaru a'alamun-Nubala,
juzi'i na 8, shafi na 335.
ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻣﺘﻮﺍﺗﺮ ﻧﺺ ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ
ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﻓﻲ ) ﺳﻴﺮ ﺍﻋﻼﻡ
335 / 8 : ﺍﻟﻨﺒﻼء ).
DR. IBRAHIM JALO
JALINGO, dalibin Ibn
Taimiyya a akida na
kwanannan, shima ya
karyata Ibn Taimiyya
akan hadisin wilaya
(Ghadir).
Ga abinda yake cewa
lokacin da aka
tambayeshi akan
hadisin Ghadir:
"Shi wannan Hadisin
hadisi ne sahihi, ya zo
cikin Tirmizi, Hadisi na
3713, Nasaa'i, Hadisi na
8089, Ibnu Majah, Hadisi
na 121, Ahmad a wurare
da dama daga cikinsu
Hadisi na 18,502, Al-
Bazzar Hadisi na 4298,
Abu Ya'ala Hadisi na
567, Al-Haakim Hadisi
na 4577, At-Tabraani
Hadisi na 2977, Ibnu Abi
Shaibah Hadisi na
23,737. Al-baani ya
inganta shi cikin Al-
Jaami'us Sagiru Wa
Ziyaadaatuh: 11,469...".
Kokarin Ibn Taimiyya na
karyata duk hadisan da
suka zo akan falalar
Imam Ali(as) ya sa ya
karyata wannan hadisi
mai zuwa:
" ﻻ ﻳﺤﺒﻚ ﺇﻻ ﻣﺆﻣﻦ، ﻭﻻ ﻳﺒﻐﻀﻚ
ﺇﻻ ﻣﻨﺎﻓﻖ ".
Annabi(saw) ya ce da
Imam Ali(as); "Ba mai
sonka sai mai imani,
kuma ba mai kinka sai
munafiki"
Wannan hadisin ya
inganta, kuma ya zo a
littattafan Ahlus-Sunnah
da yawan gaske, kadan
daga ciki:
( 152 ) 60 / 1 : ﻣﺴﻠﻢ .
84/ 1 : ( . ﺃﺣﻤﺪ58ﺍﻟﺤﻤﻴﺪﻱ : 
114 : ( . ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ642) .
8 : . ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ3736ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ : /
115 ...).
Amma sai Ibn Taimiyya
ya karyata hadisi, ba
tare da ya kawo hujja
daga ilimin hadisi ba,
hujjarsa kawai ita ce;
wai mafi yawan
Sahabbai da Tabi'ai
basa son Imam Ali(as),
ga abinda Ibn Taimiyya
ke cewa:
" ﻓﺎﻥ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭ
ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﺒﻐﻀﻮﻧﻪ ﻭ
ﻳﺴﺒﻮﻧﻪ ﻭ ﻳﻘﺎﺗﻠﻮﻧﻪ .
5 ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ - ﺝ ) /
42 ﺹ ).
"Da yawa daga cikin
Sahabbai da Tabi'ai sun
kasance suna kin shi
(Imam Ali(as), Kuma
suna zaginsa, Kuma
suna yaƙarsa.."
(Minhajus-sunnatin
Nabawiyya - (Juz'i na 5,
shafina 42).
Kokarin Ibn Taimiyya na
karyata ingantaccen
hadisi da ra'ayinsa ya sa
ya fada tarkon kafirta
Sahabbai da Tabi'ai da
munafuntar da su. Idan
aka ce da yawa daga
cikin Sahabbai suna kin
Imam Ali(as), hakan
daidai yake da ace da
yawa daga cikin
Sahabbai Munafukai ne,
Saboda ya inganta
Manzon Allah(saw) Ya
fada wa Imam Ali(as)
cewa:
ﻻ ﻳﺤﺒﻚ ﺇﻻ ﻣﺆﻣﻦ، ﻭﻻ ﻳﺒﻐﻀﻚ )
ﺇﻻ ﻣﻨﺎﻓﻖ ).
(Babu mai Sonka sai
Mumini, Kuma babu mai
ƙinka sai Munafiki).
Haka ma Idan aka ce:
da yawa daga cikin
Sahabbai suna zagin
Sayyadi Ali(as) - kamar
yanda Ibni Taimiyya ya
ce - to hakan daidai
yake da ace: da yawa
daga cikin Sahabbai
suna zagin Allah da
Annabi(saw), Saboda
Manzon Allah(saw) ya
ce:
"...Duk wanda ya zagi
Ali(as) to ni ya zaga,
wanda kuma ya zageni
to Allah ya zaga..."
Ga nassin hadisin
dirayatan, kamar yanda
Ummul-Mu'uminin
Ummu Salma ta riwaito:
" ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﻴﺮ، ﻗﺎﻝ
: ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺇﺳﺮﺍﺋﻴﻞ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ
ﺇﺳﺤﺎﻕ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻬﺎﻟﺠﺪﻟﻲ
ﻗﺎﻝ : ﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﺃﻡ ﺳﻠﻤﺔ
 ﻓﻘﺎﻟﺖ ﻟﻲ : ﺃﻳﺴﺐ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ( ﻓﻴﻜﻢ، ﻗﻠﺖ
: ﻣﻌﺎﺫ ﺍﻟﻠﻪ، ﺃﻭ ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ! ﺃﻭ
ﻛﻠﻤﺔ ﻧﺤﻮﻫﺎ، ﻗﺎﻟﺖ : ﺳﻤﻌﺖ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ) ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ
ﻳﻘﻮﻝ : " ﻣﻦ ﺳﺐ ﻋﻠﻴﺎ ﻓﻘﺪ (
ﺳﺒﻨﻲ ﻭﻣﻦ ﺳﺒﻨﻲ ﺳﺐ ﺍﻟﻠﻪ ."
ﻣﺮﺗﺒﺔ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ : ﺻﺤﻴﺢ، ﺭﺟﺎﻟﻪ )
ﺛﻘﺎﺕ . ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﻟﻬﻴﺜﻤﻲ :
ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺭﺟﺎﻟﻪ ﺭﺟﺎﻝ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ
ﻏﻴﺮ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺠﺪﻟﻲ ﻭﻫﻮ
ﺛﻘﺔ . ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﺍﻟﻨﻴﺴﺎﺑﻮﺭﻱ :
ﻫﺬﺍ ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻻﺳﻨﺎﺩ ﻭﻟﻢ
ﻳﺨﺮﺟﺎﻩ، ﻭﻗﺪ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻨﺪ ﺍﻻﻣﺎﻡ
3 : . ﺍﻟﻤﺴﺘﺪﺭﻙ323/ 6ﺃﺣﻤﺪ : 
/121. 42 : ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺩﻣﺸﻖ/
266. 130/ 9 : ﻣﺠﻤﻊ ﺍﻟﺰﻭﺍﺋﺪ.
301 ﺻﻔﺤﻪ ).
Sannan Idan aka ce: da
yawa daga cikin
Sahabbai suna yakar
Ali(as) to hakan daidai
yake da ace: da yawa
daga cikin Sahabbai
kafirai ne, Saboda
Manzon(saw) Allah
yace:
( ﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﺴﻮﻕ ﻭﻗﺘﺎﻟﻪ
ﻛﻔﺮ ).
(Zagin Musulmi
Fasikanci ne, yakar
Musulmi Kafirci ne).
Koda ka 'Dauki Imam
Ali(as) a gama-garin
Musulmi to yakarsa
kafirci ne inji
Manzo(saw). Doriya
akan ingantattun hadisi
sai da suka nuna cewa
duk wadanda suka yaki
Imam Ali(as) a Jamal,
Siffin, Nahrawan... duk
azzalumai ne. Misali,
hadisin Fi'atul-bagiya...
Idan har cewar da Ibn
Taimiyya ya yi da yawan
Sahabbai suna kin
Ali(as); alhali
Annabi(saw) ya ce kin
Ali(as) Munafinci ne,
Idan siffata Sahabbai da
Munafinci ba zagi ba ne,
to Menene zagi? Kenan
dai Ibn Taimiyya shima
yana zagin Sahabbai?
Kuma shi Muslim da
sauran malaman Ahlus-
Sunnah da suka riwaito
hadisin, suma duk suna
zagin Sahabbai?
Wani rashin adalci da
Ibn Taimiyya ya shahara
da shi shine yiwa
malamai karya, misali, a
littafinsa Minhajus-
Sunnah, da ya rubuta
don yiwa Allama Al-Hilli
radda wa littafinsa
minhajul-karama, sai
kaji Ibn Taimiyya yace
Allama Al-Hilli yace
kaza, alhali idan kaje ka
duba minhajul-karama
sai ka tarar Ibn Taimiyya
karya yake jinginawa
Allama Al-Hilla, ko ka
tarar Allamah Al-Hilli
yayi gabas, Ibn Taimiyya
yayi yamma. Don haka
malamai ke cewa; Ibn
Taimiyya a saman iska
yake sakin kalamansa
ba tare da hujja ko dalili
ba.
Wai me Imam Ali(as)
yayiwa Ibn Taimiyya
yake kinsa sa haka? Ko
dai Ibn Taimiyya
munafiki ne? Don
samun amsar wannan
tambayar bari muji me
dalibin Ibn Taimiyya a
akida; Ibn Hajar Al-
askalani yake cewa:
ﻳﺨﺘﺼﺮ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﺭﺃﻳﻬﻢ ﻓﻴﻪ ﻓﻲ
ﺍﻟﻨﺺ ﺍﻟﺘﺎﻟﻲ، ) ﺍﻟﺪﺭﺭ ﺍﻟﻜﺎﻣﻨﺔ ﻓﻲ
ﺃﻋﻴﺎﻥ ﺍﻟﻤﺎﺋﺔ ﺍﻟﺜﺎﻣﻨﺔ ( ﻋﻦ ﺍﺑﻦ
ﺗﻴﻤﻴﺔ :
ﻭﺍﻓﺘﺮﻕ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻪ ﺷﻴﻌﺎ ) :
Mutane sunyi sabani
akan Ibn Taimiyya,
ﻓﻤﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﻧﺴﺒﻪ ﺇﻟﻰ
 ( ﺍﻟﺘﺠﺴﻴﻢ ﻟﻤﺎ ﺫﻛﺮ ﻓﻲ1) 
ﺍﻟﻌﻘﻴﺪﺓ ﺍﻟﺤﻤﻮﻳﺔ ﻭﺍﻟﻮﺍﺳﻄﻴﺔ
ﻭﻏﻴﺮﻫﻤﺎ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﻛﻘﻮﻟﻪ :
1. Wasu suna ganin Ibn
Taimiyya ya mayar da
Allah jiki, kamar yanda
yake a littafan tauhidin
Ibn Taimiyya. Saboda
yana cewa:
ﺇﻥ ﺍﻟﻴﺪ ﻭﺍﻟﻘﺪﻡ ﻭﺍﻟﺴﺎﻕ ﻭﺍﻟﻮﺟﻪ
ﺻﻔﺎﺕ ﺣﻘﻴﻘﻴﺔ ﻟﻠﻪ، ﻭﺃﻧﻪ ﻣﺴﺘﻮ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺮﺵ ﺑﺬﺍﺗﻪ، ﻓﻘﻴﻞ ﻟﻪ :
ﻳﻠﺰﻡ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺘﺤﻴﺰ ﻭﺍﻻﻧﻘﺴﺎﻡ .
ﻓﻘﺎﻝ : ﺃﻧﺎ ﻻ ﺃﺳﻠﻢ ﺃﻥ ﺍﻟﺘﺤﻴﺰ
ﻭﺍﻻﻧﻘﺴﺎﻡ ﻣﻦ ﺧﻮﺍﺹ ﺍﻷﺟﺴﺎﻡ .
ﻓﺎﻟﺬﻡ ﺑﺄﻧﻪ ﻳﻘﻮﻝ ﺑﺘﺤﻴﺰ ﻓﻲ ﺫﺍﺕ
ﺍﻟﻠﻪ .
"Allah yana da hannu,
kafa, kori, fuska... na
hakika (ba tawili)..."
 ( ﻭﻣﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﻳﻨﺴﺒﻪ ﺇﻟﻰ2) 
( ﺹ ) ﺍﻟﺰﻧﺪﻗﺔ ﻟﻘﻮﻟﻪ : ﺇﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﻻ ﻳﺴﺘﻐﺎﺙ ﺑﻪ، ﻭﺃﻥ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ
 ﺗﻨﻘﻴﺼﺎ ﻭﻣﻨﻌﺎ ﻣﻦ ﺗﻌﻈﻴﻢ ﺍﻟﻨﺒﻲ(
ﺹ ( ﻭﻛﺎﻥ ﺃﺷﺪ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻲ
ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻨﻮﺭ ﺍﻟﺒﻜﺮﻱ ﻓﺈﻧﻪ ﻟﻤﺎ ﻟﻪ
ﻋﻘﺪ ﺍﻟﻤﺠﻠﺲ ﺑﺴﺒﺐ ﺫﻟﻚ ﻗﺎﻝ
ﺑﻌﺾ ﺍﻟﺤﺎﺿﺮﻳﻦ : ﻳﻌﺰﺭ . ﻓﻘﺎﻝ
ﺍﻟﺒﻜﺮﻱ : ﻻ ﻣﻌﻨﻰ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ
ﻓﺈﻧﻪ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺗﻨﻘﻴﺼﺎ ﻳﻘﺘﻞ ﻭﺇﻥ ﻟﻢ
ﻳﻜﻦ ﺗﻨﻘﻴﺼﺎ ﻻ ﻳﻌﺰﺭ .
2. Wasu kuma suna
ganin Ibn Taimiyya
marar addini ne
kacokaf, saboda ya
(nuna Annabi(saw)
mutum ne kamar kowa)
don haka ba a tawassuli
da Annabi(saw)....
 ( ﻭﻣﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﻳﻨﺴﺒﻪ ﺇﻟﻰ3) 
ﺍﻟﻨﻔﺎﻕ - ﻟﻘﻮﻟﻪ ﻓﻲ ﻋﻠﻲ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ
3. Wasu kuma suna
ganin Ibn Taimiyya
munafiki ne, sabida
kiyayyarsa wa Imam
Ali(as) da wasu
muhimnan Sahabbai.
Misali Ibn Taimiyya ya
ce:
- ﻭﻟﻘﻮﻟﻪ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻣﺨﺬﻭﻻ ﺣﻴﺚ ﻣﺎ
ﺗﻮﺟﻪ ،
"Imam Ali(as) yayi
muhawala bayyi nasara
ba (duk yakin da Imam
Ali(as) yayi baya nasara.
.."
Sannan Ibni Taimiyya
yace:
- ﻭﺃﻧﻪ ﺣﺎﻭﻝ ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ ﻣﺮﺍﺭﺍ ﻓﻠﻢ
ﻳﻨﻠﻬﺎ ،
- ﻭﺇﻧﻤﺎ ﻗﺎﺗﻞ ﻟﻠﺮﻳﺎﺳﺔ ﻻ ﻟﻠﺪﻳﺎﻧﺔ ،
- ﻭﻟﻘﻮﻟﻪ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﺮﻳﺎﺳﺔ ،
"Imam Ali(as) yayi ta
neman khalifanci bayyi
nasara ba, kuma yana
da son shugabanci,
kuma yayi yaki don
neman shugabanci.
 ( ﻭﺃﻥ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻛﺎﻥ ﻳﺤﺐ4) 
ﺍﻟﻤﺎﻝ،
 ( ﻭﻟﻘﻮﻟﻪ ﺃﺑﻮ ﺑﻜﺮ ﺃﺳﻠﻢ ﺷﻴﺨﺎ5) 
ﻻ ﻳﺪﺭﻱ ﻣﺎ ﻳﻘﻮﻝ ،
 ( ﻭﻋﻠﻲ ﺃﺳﻠﻢ ﺻﺒﻴﺎ ﻭﺍﻟﺼﺒﻲ6) 
ﻻ ﻳﺼﺢ ﺇﺳﻼﻣﻪ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻝ ،
Ibn Taimiyya yace;
Khalifa Usman yana da
son dukiya. Khalifa
Abubakar ya musulunta
yana tsoho, yayinda bai
san me yake ba, shiku
Imam Ali(as) ya
musulunta yana yaro,
kuma imanin yaro bai
inganta.
Tunda wannan hadisin
ya inganta, cewa ba mai
kin Imam Ali(as) sai
munafiki:
ﻭﻻ ﻳﺒﻐﻀﻚ ﺇﻻ ﻣﻨﺎﻓﻖ .....
Kenan da Ibn Taimiyya
munafiki ne? Tunda
baya son Imam Ali(as).
Don haka ake kiran Ibn
Taimiyya:
ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺷﻴﺦ ﺍﻷﻭﺛﺎﻥ ﻭﺷﺮﺥ
ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺷﻴﺦ ﺍﻟﻮﻗﻮﻉ ﻓﻲ
ﺍﻟﺨﻠﻔﺎء ﺍﻟﺮﺍﺷﺪﻳﻦ.


DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


Ma'asumah Nigeria
news update.

Fertymerh Shaheder

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post