@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A KASHE SHI KO KUMA A TSIRE SHI
Yana daga cikin illolin rashin yin hukunci da littafin Allah kaga ana kashe wanda ba shi da haqqin komai, wanda ke da haqqin kisa a kansa kuma ya zama shine mai zartar da hukuncin kisa kan wanda bai ji ba bai gani ba (innocent ).
Umarnin Allah cikin hadisil-Qudsi inda yake cewa:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ DUK WANDA YAYI ADAWA DA MASOYINA, TO, NA YI MASA IZNIN SHIRIN YAQI DANI .‘’
Kuma duk wanda ya yaqi Allah da Manzonsa (S.A.W.W , san nan ya kasance mai yin barna a doron qasa, to, hukuncinsa shine kisa ko a tsire shi ko kuma a kore shi daga cikin qasar.
Tabbas, babu mai yaqar Allah kamar wada ke kashe bayin Allah muminai masu qoqarin tabbatar da tsarin Allah ya kasance shine mai iko a doron qasa.
Ga abinda Allah ke fada a kansu cikin littafinsa mai tsarki:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ ABIN SANI KAWAI, SAKAMAKON WADANDA KE SUKE YAQAR ALLAH DA MANZONSA, KUMA SUNA KAI KAWO CIKIN QASA DOMIN BARNA, A KASHE SU KO A TSIRE SU, KO KUMA A YANYANKE HANNAYENSU DA QAFAFUWANSA DAGA SABANI, KO KUMA,A KORE SU DAGA QASA. HAKAN GARE SU WULAQANCI NE A CIKIN RAYUWAR DUNIYA , KUMA A LAHIRA SUNA DA WATA AZABA MAI GIRMA !‘’
(MA'IDA:aya ta 33).
Na'am, tare da cewa ana cewa wannan hukunci ne na masu yin fashi da makami, amma cikin hukuncin za muga akwai kisa.
Shi kuma kisa hukunci ne na wanda ya kashe rai bisa ganganci don ta'addanci. Idan kuwa haka ne ai babu makashin rai kuma mai barna cikin qasa kamar Buhari , musamman ma cikin wannan qarni.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~7th February, 2020.
Tags:
Tunatarwa
ALLAH (TA) YAGAGGAUTA KWATO MANA SU SAYYEED (H) YABASU LAFIYA YAKUNTATAWA WANDA YAKUNTATA MAKU(H) NA
ReplyDelete