Hijabin Tufafi Na Hudu (4)



Ma'asumah Nigerian News Update, tare da Bin Haroun Sigau.

HIJABIN MAZA

-Masu biye dani zasuyi mamaki suji na ambaci Hijabin Maza, amma in ka biyo zaka sami gamsuwa game da wannan sashi.

-Abu ne mai gayar muhimmanci mu jawo hankalin Maza game da yadda zasu saka sutura, duk da dai mun ambata su a rubututtukan mu da suka gabata.
Ga su kamar haka:

-Namiji wajibi ne ya rufe dukkan al'aurarsa a ko wanni lokaci a ko wanni waje, ga dukkan mutune saida matarsa da ƙaramin yaro.

-Wajibi ne ya rufe al'aurarsa yayin sallah in ba da wata lalura ba, kota rashin kamilallen sutura ko kuma wani abu makamancin haka.
-Tufafinsa kada ya zama matsattse ta yadda zai ke bayyana siffar abinda ya wajaba a rufesu.

-Kada ya zama sara-sara domin zai iya bayyana kalar fata, sabida zai iya nuna fatar jikin abinda ya kamata a sirranta su.

-Suturar kada ya zama sanannen kayan ado irin na Mata.
-Tufansa kada yazam mai daraja/tsada, na alfahari, ko jiji da kai.

-Ba'a yarje wa namiji saka kaya na gwal ba koda mara kyau ne.
-Fatan ƴan uwa na maza suma zasu kiyaye da waɗannan janibobin.
-Rubutu na gaba kuma wanda zai zama na ƙarshe, shine; m
Muhimmancin Hijabi.

┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post