@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHI FA TAIMAKON ZALUNCI ZALUNCI NE
Yin karatu a kowanne fanni na ilimin zamani ko na addini ba zai taba zama haramun ba, sai dai yadda za ayi aiki da ilimin ne zai iya zama haram matuqar ba a kiyaye dokokin Allah cikinsa ba.
Ko da Qur'ani mutum ya karanta, amma sai ya yi aiki da ilimin Qur'anin nasa ya lullube gaskiya ko ya taimaki zalunci, to, wannan karatu nasa zai zame masa jagora zuwa wuta. Haka ma yake cikin ilimin alqalanci ko lauya, wanda yayi aiki da wannan ilimi wajen taimakon gaskiya da mai gaskiya zai sami daukaka a wajen Allah da kuma mutunci da samun yabo daga jama'a.
Allah (T )ya gargade ku alqalai da lauyoyi kan cewa kada kuyi amfani da wannan ilimi naku wajen taimakon azzalumai da suka ha'inci kansu.
Ga dai gargadin da yake muku cikin alqur'ani :
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KUMA KADA KAYI JAYAYYA (don tunkude mummunan aiki )DAGA WADANDA SUKA HA'INCI KANSU (ta hanyar zalunci ). LALLE ALLAH BA YA SON WANDA YA KASANCE MAI HA'INCI MAI YAWAN ZUNUBI.
SUNA NEMAN BOYEWA(ta'addancin da suka yi)DAGA MUTANE KUMA BA SU NEMAN BOYEWA GA ALLAH, ALHALI KUWA SHI(Allah )NA TARE DA SU A LOKACIN DA SUKE KWANA DA NIYYAR YIN ABINDA (Allah )BA YA YARDA DA SHI (na ta'addancin da suke qullawa )DAGA MAGANA . KUMA ALLAH YA KASANCE MAI KEWAYEDA (sanin )ABINDA SUKE AIKATAWA (na sharri da nufin zalunci ).
GA KU, YAA WADANNAN(Alqalai da Lauyoyi , KUN YI JAYAYYA (da gaskiya )DOMIN TUNKUDE MUSU (kunya )A CIKIN RAYUWAR DUNIYA, TO, WANENE (daga cikin ku )WANDA ZAI YI JAYAYYA (a yau )DOMIN TUNKUDE MUSU (wannan abinda suka aikata )A RANAR,QIYAMA?KO KUMA WANENE (daga cikin ku )ZAI KASANCE WAKILI A KANSU?‘’
(Suratul-Nisa'i, aya ta 107-109).
Su fa wadannan azzalumai,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ SUNA NUFI SU BISHE HASKEN ALLAH (ne )DA BAKUNANSU, ALHALI ALLAH MAI CIKA HASKENSA NE, KUMA KO DA KAFIRAI (da azzalumai da munafukai )SUN QI !‘’
(Suratul-Saff, aya ta 8).
Saboda haka ku ji tsoron Allah ta hanyar taimakon gaskiya da me gaskiya, kuma ko da wanne addini ka ke yi ba, domin babu addinin da ke goyon bayan zalunci da azzalumai .
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
~6th February, 2020.
Tags:
Tunatarwa