Hanyoyi 7 na gujewa cutar hakin wuhan (corona Virus)

Hanyoyi 7 na Gujewa Cutar Hakin Wuhan (Corona Virus)

Wannan fassara ce da nayi daga shafin likita Abdullahi Dahiru. Ina fatan mutane zasu yada saboda amfanin  alumma.

A yanzu dai ta tabbata cutar ta shigo Nigeria, bayan da aka samu wani mutimin Italy da wannan cuta a Lagos. Wanda hukumomin  lafiya na kasa da na jihar Ikko suka tabbatar. Tuni dai hukuma ta kebe wannan mutum, domin kara kula da lafiyarsa da kuma hana yaduwarta.

Ga wasu hanyoyi Bakwai da ya kamata a kiyaye domin hana  yaduwar wannan cuta acikin alumma.

1) Kar ka Razana
Farko shine, kar mutane su razana ko su kidime. A irin wannan hali, ba abinda ke sanya abubuwa su taazzara, irin kidimewar  alumma. Hakan kan sa ayi gudun gara, a fada wa zago. Kar mutane su zaci, baa warkewa, a wannan shekara kawai sama da mutane Dubu Talatin ne suka warke daga wannan cuta a duk fadin duniya

Kasar Nigeria ta taba shiga irin wannan hali a kan cutar Ebola, kuma Allah cikin ikonsa aka shawo  kan ta. Wanda a zahiri ma tafi wannan cuta ta Corona hadari. Amma bisa ga yardar Allah da himmar hukumomin lafiya aka shawo kan ta. Hasashe ya nuna, cutar Hakin Wuhan (Corona) ka iya kashe kashi 2.3% ne na wanda suka kamu, kafin a shawo kan ta. Inda Ebola kan kashe kashi 90% na wadanda suka kamu kafin a shawo kan ta.  To in dai hukuma ta shawo kan waccan, wannan ma in an bata hadin kai zata zama tarihi. Don haka babban abu dai kar mutane su razana da cutar !!

2) Wanke Hannu
Hukumar lafiya ta jawo hankalin mutane akan su tabbatar da wanke hannayensu akan kari. Su tabbatar sun wanke su tas, da Sabulu. In da hali, ayi amfani da Sabulu wanke hannu na zamani wato Hand Wash (wanda kwalbar tasa ba wani tsada gare Shi ba). Inda hali,  a jaddada wankewar a duk lokacin da aka samu dama.

3) Ka Nisanci mai yawan tari ko atishawa

Ka nisanci wanda kaga yana yawan tari ko atishawa da akalla rabin mita, kwatankwacin kafa 5. Wadannan sune alamun farko na kamuwa da cutar.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa, a yayin da mai cutar yayi tari ko atishawa,  yakan fitar da wani ruwa, wanda ke dauke da kwayoyin cutar. Saboda haka, in kana kusa, zaka iya daukar wannan cuta daga wannan ruwa da ya fito.

4) Kauracewa Tarurruka
Akwai bukatar mutane da ke yawan tari da su kauracewa shiga cikin taro, saboda kar su yada cutar. Ya kamata su zauna a wuri daya, inda zaa kula da lafiyarsu.
Duk wanda ke yawan tari , ko atishawa ya kamata ya kauracewa shiga mutane, ya kuma yi kokarin Kai kansa asibiti, domin a duba lafiyarsa, ba tare da bata lokaci ba.

5) Kula da Yadda Kake Numfashi

Ka tabbata mutanen da ke tare da kai suna rufe hanci da bakinsu, a lokacin da zasu/suke tari. In da hali, mutane su ringa amfani da hankici,  suna kare hanci da bakinsu, a kowane lokaci.

In kuma ba hali, yi tarin acikin hannun rigarka ko tafin hannunka, ko kuma toilet paper. Ka tabbata ka yadda ta a shara,  bayan kayi amfani da ita.

6) Ka Zauna a Wuri Guda in ka Kamu da Cutar

Ka zauna wuri guda in ka kamu da cutar, musamman in ka fara ganin alamun cutar, wadanda suka hada da : Zazzabi, tari, haki, da sauransu.

Tuntubi hukumomin  lafiya mafi kusa a yayin da ka ga alamun cutar tare da kai.

8) BABU WANI MAGANIN GARGAJIYA KO NA MUSULUNCI DA YAKE MAGANIN CUTAR CORONA, KAR KA YADDA A DAMFARE KA. KA GARZAYA ASIBITI CIKIN GAGGAWA, A YAYIN DA KAGA ALAMUN CUTAR A TARE DA KAI.

JAMAA MUYI HATTARA!!!

Allah ya bamu lafiya da zama lafiya!!
Ilaheeey ya rab.

Danna Jan Rubutun nan Domin samun Rubuce-rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post