@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ABINDA WASU SUKA JAHILTA KENAN .
Hada salloli biyu a lokaci guda bai kasance wani baqon abu wajen ma'abuta ilimi ba. Sai dai abinda wasu ke gani ko cewa shine, hada su a lokaci guda ba ya halatta a halin zaman gida matuqar ba bisa wani uzuri ba.
Abinda suke cewa game da wannan hukunci shine, yin hakan na halatta ne kawai a halin tafiya (SAFARI )ko kuma a halin tsoro (KHAUF )ko kuma bisa wata lalura ta ruwa ko duhu ko laka (mud ) . Shine suke ganin masu hada salloli biyu a halin zaman gida ba tare da wani uzuri ba a matsayin masu sabawa dokar Allah ko sunnar Annabi (S.A.W.W ).
Sai dai kuma ilimi ne mai hukunta komai ba wai ra'ayin wasu ko ganin dacewar abu ba.
Ya tabbata cikin hadisin Manzon Allah (S.A.W.W )cewa yana hadawa ko ya hada ba tare da wani dalili irin wanda wasu ke cewa ba.
Ga hadisin nan kamar haka:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
An bani labari daga Malik, daga baban Zubairi Al-Makiyyi, daga Sa'id Bn Jubair ,daga Abdullah Bn Abbas (R.A )yace:
‘’ MANZON ALLAH (S.A.W.W )YA SALLACI AZAHAR DA LA'ASAR A HADE, DA MAGRIBA DA ISHA'I A HADE , BA TARE DA TSORO BA KUMA BA A HALIN TAFIYA BA .‘’
-Muslim ya fitar wannan hadisin cikin sahihinsa hadisi me lamba: 289.
- Muwadda Malik, hadisi ne lamba: 329.
(KITABUL QASARUS-SALATI FEE SAFRIN, BABUL JAM'I BAINA SALATAINIY FIL HADHARI WAS-SAFARI ).
Sai dai shi Imam Malik ya kawo wani tawili inda yake cewa: ‘’ AMMA INA GANIN HAKAN KAMAR ANA RUWA NE .‘’
Amma da aka tambayi Ibn Abbas (R.A )dalilin hada sallar da Annabi (S.A.W.W ) yayi, sai yace:
‘’ YA YI HAKANNE KAWAI DON KADA A QUNTATAWA MUTUNE .‘’
Ma'ana, babu wani dalili na ruwa ko wani abu kamar yadda Imam Malik ke zato, sai dai kawai an bawa mutane ne damar yin haka ga mai ra'ayin hadawa.
Wannan dalili yasa kuke ganin 'yan shi'ah na hada sallolinsu a wasu lokuta.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~17th February, 2020.
Tags:
Taskar ilimi