@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHINE WANDA BA A YIN NADAMA DA AURENSA.
Aure ibada ce daga cikin ibadun da Allah ya sharadanta mana, sannan ya sanya,dokoki cikinsa don samun albarka da kuma natijar da ke cikinsa.
Ibada ce wacce ake samun dimbin lada cikinsa matuqar an kiyaye dokokin dake cikinsa. Sannan akan sami zunubi, kuma yakan yi sanadin tafiyar mutum zuwa wuta matuqar ba a kiyaye dokokin dake cikinsa ba.
To, a matsayin ka na mahaifin yarinya yana da kyau kayi dubin wanda ya kamata ya aurin 'yarka, don kare mutuncinta da kuma naku, da kuma tsare dokokin Allah wanda ya kasance gare shi muke komawa baki daya.
Imam Hussaini (A.S )yayi mana nuni mai kyau zuwa ga wanda yafi dacewa da auren 'ya'yayenmu mata. Matuqar mun bi wannan shawaa tasa, haqiqa za muga aikhairi cikin aurar da 'ya'yayenmu mata.
Wata rana wani mutum ya zo wajen Imam Hussaini (A.S )sai yace masa;‘’ Lalle ni ina da 'ya (mace ), amma wa kake gani (ya fi dacewa )na aurar masa ?‘’
Sai Imam (A.S )yace:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KA AURAR DA ITA GA ME TSORON ALLAH (T ), DOMIN IDAN YA SO TA ZAI KARRAMATA, IDAN KUMA YA QITA (saboda wasu munanan halayenta )BA ZAI ZALUNCETA BA.‘’
(Al-Mustazraf, J:2, SH:218 ).
Idan muka nazarci wannan hadisi kuma muka yi la'akari da yanayin dabi'un mutane da kuma abinda suka fi rinjaye kansa za mu gaskata cewa tabbas ita zuciya ta fi kyautatawa abinda take so, sannan kuma ba ta cika kyautatawa abinda ba ta so ba, maimakon kyautatawar ma sai kaga cutar da wannan abin ake yi. Wannan kuwa dabi'ar zuciya ce wanda babu mai musanta haka .
Amma shi mumini ba haka yake ba, ko da kuwa ba ya son mutum ya irin yanayin dabi'a ta zuciya , to, ba zai zalunci wannan abin ba . Idan kuma ya kasance abinda yake so ne, to, zai karrama shi ko girmama shi fiye da yadda kowa zai yi.
Sai dai kuma yanzu ba wannan ne tunanin mafi yawan iyaye ba, domin su sun fi hangen gyalgyalin duniya wajen samarwa 'yarsu mijin aure, ko da kuwa shi wannan mutumin azzalumi ne ko fasiqi ne , matuqar yana da abin hannu shike nan ya zama wanda ake kira ko fatan zuwansa ga 'ya.
Su kuwa irin wadannan mutane ba su cika girmama mace ba, domin suna gani za a so don abin hannusu. Kuma irinsu ne idan wata matsala ta auku tsakanin su da matansu sai suyi musu walaqancin fa har iyayen su ma,sai sun girgiza.
Saboda haka mu bi shawarin bayin Allah don hutacar da zukatan mu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~11th February, 2020.
Tags:
Taskar ilimi