@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KAI DAI KAYI KOMAI NAKA DON ALLAH .
'Dabi'ar dan Adam haka take, kowa da irin tunaninsa. Za ka iya samun mutum na aikata daidai, amma kai a wajenka ba daidai bane komai bayanin da za ayi maka don ka fahinta.
Wani kuma za ka tarar ba daidai yake ba, amma kai a wajenka babu mai aikata daidai kamarsa , bisa dogaro da fahintarka ko tunaninka.
Irin wannan tunani ko fahinta na jagula al'amra, domin ta dalilil irin wannan tunani naka za ka iya gina wasu a kansa, har su kasance ba sa fahintar komai in ba tunaninka ba.
A lokacin da Allah (T )ya aika Musa (A.S )da shiriya zuwa ga Fir'aina, mafi yawa daga mutanen Fir'auna ba su yarda da abinda Musa (A.S )yazo u da shi na shiriya ba.
Har ma Fir'auna yake cewa mutanensa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
‘’ BA NI NUNA MUKU KOMAI FACE ABINDA NA GANI, KUMA BA NI SHIRYAR DA KU SAI GA HANYAR SHIRYUWA.‘’
(SURATUL-GHAFIR, AYA TA 29).
Ka ga a tunaninsa Musa (A.S )ne akan bata, shine yake kan tafarkin shiriya .
Ko a lokacin da Manzon Allah (S.A.W.W )ya fara da'awarsa ta cewa abin bauta daya (1)ne shine Allah, sai mafiya yawa suka riqa gani tamkar wata hauka ce ma ta shafe shi, sune masu tunani kyakkyawa na ganin bai kamata ace abin bauta daya ne ba . Kan haka su kayi ta aibanta da'awar tasa.
A wannan zamani an sami wata da'awar kafa shari'ar muslimci a wata jiha da ake kira Zamfara (GUSAU ). Kunga wannan mummuniyar fahinta ce ko tunani domin tun farko an kaucewa ASAS . Amma abin mamaki shine, manyan mutane masu rawunna da sunan malanta duk suka juya akalarsu zuwa gare shi suna ganin shine masoyin addinin muslimci wanda zai kafa shari'a cikin sauqi.
Kan haka suka riqa aibanta mai da'awar gaskiya SAYYID ZAKZAKY (H )kan cewa ashe dama ba shari'ar muslimci yake son kafawa ba tunda yana adawa da shari'a Bazamfariya, amma yanzu ya al'amarin ya kasance ?
Wa aka gano cewa shine akan daidai ko da kuwa an qi sallama masa?
ALLAH YA 'DORAMU KAN FAHINTAR GASKIYAR .
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
07059911360-09039791509
~19th February, 2020.