Dalilin da ya hana Imam Ali (As) yaƙar shuwagabannin farko!!!



DUKKAN A'IMMA (A.S )ABIN KOYI NE GARE MU

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Dalilin wannan rubutu nawa shine, subhar da 'yan'uwanmu Ahlus-Sunnah ke kawowa ne don qalubalantar mu 'yan Shi'a kan cewa wanene yayi daidai tsakanin Imam Ali da Imam Hassan da Imam Hussaini (A.S )bisa yadda kowa yayi a zamaninsa?

To, amsar wannan abu a fili yake, domin aikin kowa daga cikinsu bisa nassi yayi shi.

  IMAM ALI (A.S )

Riwaya daga Abdullahi Bn Imam Ahmad yace;Muhammad Bn Abubakar Al-Mu'adamiy ya bamu labari , Fudhail Bn Sulaiman An-Numairi ya bamu labari, Muhammad Bn Abiy Yahya ya bamu labari daga Iyasin Bn Amruu Al-Aslamiy daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A.S )yace, Manzon Allah (S.A.W.W );

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE DA SANNU WANI SABANI KO AL'AMARI ZAI KASANCE (a bayana ), IDAN DAI KANA DA IKON SAMAR DA ZAMAN LAFIYA YA KASANCE, TO, KA AIKATA.‘’

(Musnad Ahmad, J:1, SH:90)

Wannan khudubar ce tasa yayi haquri da su a haka don samun zaman lafiya ba wai don sun aikata daidai ba.

IMAM HASSAN (A.S )

Baban Bakrata ya bada labari cewa, wata rana Annabi (S.A.W.W)ya fito da Hassan sai ya hau kan Mimbari da shi sannan yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ WANNAN 'DAN NAWA SHUGABA NE, DA SANNU ALLAH ZAI SULHUNTA TSAKANIN RUNDUNA BIYU DA SHI DAGA MUSULMAI.‘’

(Bukhari, hadisi me lamba 3629)

Kenan sulhu da yayi da Mu'awiyyah bisa yardar Allah ne don cigaban muslimci kamar yadda babansa Imam  Ali (A.S )yayi .

DAANNA NAN:-  ziyarce mu a shafin Facebook

IMAM HUSSAINI (A.S )

Ruwaya daga Baghwiy, daga Ummus-Salama (R.A )tace; Jibril (A.S )na tare da Manzon Allah (S.A.W.W ) Hussaini kuma na tare dani , sai na gafala da shi, sai ya (rarrafa )ya tafi wajen Annabi (S.A.W.W ), sai Annabi (S.A.W.W )ya dauke shi ya dora shi akan cinyarsa. Sai Jibril (A.S )yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KANA SONSA NE YAA MUHAMMAD ?‘’ Yace, ‘’ EH.‘’

Sai yace; ‘’ LALLE DA SANNU AL'UMMARKA ZA TA KASHE SHI, INDAN KANA SO SAI NA NUNA MAKA QASAR DA ZA A KASHE A ITA. ‘’

Sannan ya shimfida fikafikansa akan qasa ya nuna masa wata qasa , ana cewa mata ;KARBALA'A (baqin ciki da bala'i ). Wata qasa ce ja (red )a wajen Iraqi (out of Iraq ).

(Nurul-Absar, SH:204).

Saboda haka kowa daidai yayi bisa nassi daga Annabi (S.A.W.W ). Sannan hakan ba yana nuna cewa wadanda aka bari ba a yaqe su ba, ko wadanda akayi sulhu dasu akan daidai suke ba.

Daga wakilanmu na  Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

08137925034-07059911360

~21th February, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post