DAGA BAKIN SAYYEED ZAKZAKY (H)

*Jagora (H) Yace:*

"Ka gane wannan al’amari fa, mu aka kawo ma hari, aka bude mana wuta, aka harbe mu da bindiga, aka kashe mutane sama da 1,000 ciki har da 'ya’yanmu.

"Ni da matata an harbe mu, ni an ja ni a kan gawar ‘ya’yana ne. Sannan kuma aka kawo mu nan aka kulle duk cikarmu da harsasai a jikinmu. Yanzu haka muna fama da ciwo duk jikinmu da harsasai.

“To, sannan mu muka kai kara kotu, muka ce don me ake tsare da mu? Suka tura lauyan gwamnati, yace suna tsare da mu ne domin su kare mu.

"Kotu bayan ta gama jin kowanne bangare ta fitar da hukunci, cewa, lallai ba wata doka a Nijeriya ko wacce Nijeriya ta saka ma hannu (ta kasar waje) wacce ta ba da dama gwamnati ta tsare wani mutum da sunan tana kare shi. Saboda haka (Kotu) ta hukunta cewa a sake mu ba tare da gindaya sharadi ba.

"Yau an kwashe kusan shekara da watanni shiru, ba su bi umurnin wannan kotun ba. Sannan kuma yanzu ka zo kace wai ka kawo za a kai ni kara? Wannan bai da ma’ana ai.”

— Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), lokacin da aka ce Gwamnatin Kaduna za ta kai shi kotu bayan tsarewar da akai masa a Abuja na fiye da Shekaru biyu a hannun DSS, alhali kotu ta ba da umurnin sakinsa, gwamnatin Buhari ta ki bi.

Danna Jan Rubutun nan Domin samun Rubuce-rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post