Da'awar Sheikh Zakzaky (H)..




@Ma'asumah Nigerian News Update@

 Gwagwarmaya: Kalma ce dake nufin fafutuka domin ganin wani abu ya tabbata. Misalin fafutukar ganin an samu Ilimi ingantacce, ko kuma kau da jahilci daga cikin Al'umma. Shi maulana Sheikh Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H) yana da'awa ne bisa fafutukar (Gwagwarmaya) ganin addinin Musulunci yayi iko da matafiyar rayuwarmu, da kuma tunkude zalunci daga doron kasa.

 Mazhaba: Zamu iya cewa Mazhaba wasu duwatsu guda uku ne da aka aza sanwar Musulunci a kai wato Akida, Furu'a (Mazhaba) da kuma Tasauwuf (Sufanci ko Irfani). A takaice dai Mazhaba na nufin fahimtar (Fiqhu) yanda ayyuka zasu kasance, don haka akwai mazhabobi masu yawa.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

 Mazhabiyya bata wadatarwa ba tare da gwagwarmaya ba. In mun lura da Imam Khomein (QS) ai akwai Mazhaba a kasarsa, amma a hakan ya mike da Gwagwarmaya.
 A takaice Gwagwarmaya shine tubali wanda  Mazhaba take tsayuwa akansa, idan gwagwarmaya ta rushe to Mazhaba bata da amfani.

 Ita da'awar Sheikh Zakzaky Gwagwarmaya ce, mazhabiyya a uslubin da'awar Allama (H) zabi ce, babu tilas ko kuma kira a koma kanta. Yana kira ne ga al'umma suzo a hada kai domin kawar da zalunci da tabbatar da adalci, wannan kuma abu ne da kowane Dan Adam yake so. Ba kira yake zuwa ga dole azo ayi shi'a ba, amma azo ayi Gwagwarmayar Addini.

Daga Wakilinmu,
 — Ibrahim Almustapha Saminaka
 - 13/January/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post