@Ma'asumah Nigerian News Update@
Fadar shugaban Najeriya ta ce ta ji yadda wani rukunin mutane suka yi wa tawagar Shugaba Muhammadu Buhari ihu a yayin da ya kai ziyarar jaje a Maiduguri.
Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa, wanda ya dauki bidiyon da ya bazu a shafukan intanet da ke nuna ana yi wa Buhari ihu bai a yi wa mutanen Borno adalci ba — wadanda ya ce an san su da karamci da son baki.
"Da ni aka shiga gari [Maiduguri] tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Shehun Borno kuma jama'a ne suka fito suna cewa sun gode suna ala san barka."
"Amma akwai wata matattara da suke cewa ba sa so, kuma ni ma na ji da kai na masu cewa ba sa so," in ji Garba Shehu.
- DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Buhari dai ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa harin Auno da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 30 raar Lahadi.Wasu dai na ra'ayin cewa ihun da aka yi wa shugaban manuniya ce kan yadda al'ummar arewa maso gabashin kasar suka fusata da rashin daukar kwakkwaran mataki daga gwamnatin don kawo karshen hare-haren Boko Haram.
Daga wakilanmu
Bin Haroun Sigau.
Tags:
Labaran Duniya