Daga:M.N.N UPDATES
Tare da wakilinmu:Jibril Usman Sarki
Ciwon asma wani ciwo ne na hanyar numfashi dake janyo matsalar rashin yin numfashi yadda ya kamata. Yakan janyo matsalar rasa rai ma a wasu lokutan idan abin yayi tsanani. Yawanci gadon ciwon ake, kuma wanda ya gada zai iya zama lafiya lau na tsawon wani wani lokaci kafin a gane, wato kenan yakan iya faruwa kusan ga kowa daga kowane mataki na shekaru har zuwa karshen rayuwa.
Amma a lokacin da ciwon ya motsa, kafofin shigar iskar numfashi na makogaro a jikin dan Adam kan rufe ta yadda za’a samu nauyi ko rashin dadin yin numfashi. Huhu zai samu karancin iskar da ta dace ya shaka.
Matsalar asma tana cikin matsalolin da kan hana mai fama da ita rayuwarsa ta yau da kullum, kamar zuwa aiki a ofisoshi, ko gona, ko kuma makaranta, idan dalibi ne. Asma har ila yau kan hana iyali barci isasshe da dare, kuma lokaci da dama iyaye kan rasa yin aiki da rana saboda cutar asmar ‘ya’yan su.
Su Wa Kan Yi Fama Da Cutar Asma?
Asma tana shafar kowane jinsi na mutane, farare ne ko bakaken fata, kuma a kowane mataki na shekaru cikin kowace kabila. Amma an yi amanna cewa mutane matalauta ne suka fi yawa wajen fama da wannan matsala.
Shin Wani Na Iya Daukar Cutar Daga Wani?
A’a. Asma bata yaduwa daga wani zuwa wani kamar ta hanyar barci a daki daya da mai cutar, ko cin abinci a kwano daya ko shakuwa tare da mai cutar kamar majinyaci marar lafiya, ko ta auratayya.
Shin Ko Ana Gadon Cutar?
Kwarai kuwa bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar gadon cutar tsakanin iyalai
madanganta kamar daga kakanni ko iyaye ko yayyen uwa ko na uba, ko dai daga wasu dangi na kusa.
Alamomin Asma
Alamomin asma ba a boye suke ba, kuma sun hada da:
1:Wahala a lokacin numfashi wato a rika yi sama-sama, hade da jin wata irin kara numfashin.
2:Matsanancin tari
3:Qaruwar fitar ruwan hanci, ba lalle ne a ga majina ba
4:Tsukewa ko daurewa da rashin jin walwala a qirji
Abubuwan Dake Tada Ciwon Asma
Tunda mun ce asma a kwance take tashi take jefi-jefi, an yi amanna wadannan abubuwan da zamu lissafa suna cikin muhimman abubuwan dake tayar da ciwon. Saboda haka yana da kyau a dauki matakin kariya daga su, kuma kowane mai asma ya kamata ya san me yake tayar masa da nasa, ya kiyaye shi, domin kowa da nashi abinda ke tayar da ciwon.
1:Gashin mage (idan ya bi iska aka shake shi)
2:Shakar iska mai tsananin sanyi
3:Shan taba sigari
4:Kayan rini
5:Kurar karmami
6:Hayaqi kamar na wuta ko na janareto
7:Gwajin Cutar Asma
A mafi yawan lokuta likitoci kan gane ciwon asma ta tambayoyi da sauraron karar numfashi a huhun mai matsalar, don haka ba sai sun jira gwaje-gwaje ba suke cewa ko akwai asma ko babu. A wasu lokutan akan bukaci wadannan gwaje-gwaje domin tantance karfin matsalar da nemo wasu matsalolin na daban
Awon numfashi (spirometry) inda akan binciki yawan iskar dake shiga da fita a huhu
Hoton kirji
Gwajin majinar kirji (sputum)
Awon kwayoyin jini.
Yadda Za’a Rage Ko Kawar da Cutar
Cutar asma kan sa a rasa rai idan ba’a dauki matakin da ya dace ba idan ta tashi. Yana da kyau iyali su lura cewa makasudin maganin cutar asma shine:
A kawar da dukkan alamominta
A dawo da numfashi dai-dai
Yana da kyau a san magungunan cutar
Shan magani kamar yadda likita ya bayyana
A san abubuwan dake haddasa cutar asma kamar yadda aka zayyana a sama, sannan a kawar da su ko a rage su a muhalli
Abubuwan Daya Kamata A Yi A Lokacin Da Ciwon Ya Tashi
Abu na farko shine mutun yayi kokari ya natsu, kada ya tayar da hankalinsa
A sha maganin da aka tanada da gaggawa
A mafi yawan lokuta maganin na shaka ne, don haka mutum ya tabbatar ya je an koya masa yadda ake shaka, kada yayi aikin baban-giwa
Mutun ya daure yayi ta numfashi sannu-sannu lokacin da ciwon ya tashi
Idan magungunan basu sa matsalar ta lafa ba, a garzaya asibiti mafi kusa
Ire-Iren Magungunanta
Akwai magunguna shahararru masu kwantar da ciwon nan take da masu kiyaye tashin ciwon wanda idan mutun ya je asibiti ana rubuta masa, qwayoyi kenan.
Sa’annan akwai wadanda ake shaka ko kuma zuqa ta baki (inhalers) wakanda ke aiki cikin gaggawa, suma ana iya rubutawa mutum ya saya. Suma iri biyu ne, akwai mai kwantar da ciwon in ya tashi, akwai kuma mai kiyaye tashin ciwon. Likita zai rubuta duk wadanda suka dace.
Tags:
Cuta da Magani