Coronavirus: Atiku ya bai wa Buhari shawara kan yadda za a yaki cutar a wannan ƙasa


@Ma'asumah Nigerian News Update@

Daga: Bin Haroun Sigau

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP mai hamayya ya ba gwamnatin Buhari shawarwari ciki har da soke jigilar jirage zuwa kasashen da cutar ta bulla.

A cikin wasu jerin sakwannin da ya wallafa a Twitter, Atiku ya ce yanzu da aka tabbatar da bullar coronavirus a Lagos, a matsayinsa mai kishin kasa zai ba gwamnatin Buhari shawara kan matakan da suka fi dacewa a dauka.

A ranar Alhamis ne hukumomi a Najeriya suka tabbatar da bullar cutar corona a Najeriya inda suka ce wani dan Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo daga Milan zuwa Lagos.

Atiku wanda ya sha kaye zaben 2019 kuma babban mai hamayya da Buhari, ya ce kamar yadda aka rufe iyakoki domin yakar zagon kasa ga tattalin arzikin kasa, yanzu kuma lokaci ne da ya dace a dakatar da jigilar jiragen sama zuwa kasashen da ke fama da cutar.

"Najeriya na bukatar daukar tsauraran matakai domin dakile bazuwar cutar. kuma kare rayuka ya fi ceto tattalin arziki muhimmanci"

"Yanzu babu wani batun zargi ko nuna dan yatsa ga wani. Idan ana zargi ya kamata a dakata, a mayar da hankali wajen samar da mafita." in ji Atiku.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post