CORONAVIRUS ADADIN MASU MUTUWA YANATA KARA YAWA!!

CORONAVIRUR MUTANE SUNATA KARA MUTUWA.
Hukumomin lardin Hubei da ke tsakiyar kasar China sun ce mutane 245 sun mutu daga barkewar sabuwar cutar Coronavirus da zuwa yanzu ta kashe mutane 1,367 tun daga wata Disamban bara.
Sanarwar ta sabbin adadin wadanda suka mutu tana zuwa ne bayan China ta fada jiya Laraba cewa, adadin wadanda suke kara kamuwa da cutar ya ragu a kwana na biyu a jere.
Jami’an lafiya a Hubei, da nan ne ainihin inda cutar ta barke a watannin biyu da suka gabata, sun ce canja hanyar da suke gano cutar daga aiki da dakunan gwaje-gwaje zuwa yin amfani da na’urar kwamfuta don duba jikin mutane. Canje-canjen hanyoyin gano cutar ya kara gano adadin wadanda suka kamu da cutar a duka fadin China zuwa dubu sittin (60,000).
Jiya Laraba,shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Ghebreyesus, ya bayyana farin cikin labarin raguwar kamuwa da cutar tare da matakan da aka dauka.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post