Na dauka magana ce ta yan'adawa saida naji da kunne na a BBC Hausa kafin na yarda.
Na kasance magoyin bayan shugaba buhari kuma har yanzu ina tare dashi bana kuma nadamar zabarsa, domin ko gobe zai sake takara shi zan zaba saboda ingancinsa yafi illarsa yawa. Amma :-
A hannu daya gaskiyar magana wannan gwamnati ta Buhari ita ta sayi wannan ihu da kudinta, kuma a nawa ra'ayin babu wani butulci da mutanen Maiduguri sukayi, illa dai sun nuna damuwarsu ne a zahiri.
Idan za'a iya tunawa mutanen kasar nan sun zabi wannan gwamnati ne saboda a daina kashe kashen da akeyi domin samun kwanciyar hankali, don haka baya zama uzuri ace lokacin Good luck ana kashe mutum Dari yanzu kuma ana kashe mutum goma ko ashirin a dauka anci nasara, ko kadan ba haka bane jama'a suna so ne a dakatar da kashe mutane kwata kwata, amma sai gaya abin ya gagara. A gefe daya ma wash matsalolin tsaron sun kunno kai irin na mummunar garkuwa da mutane da akeyi, Wanda ya zama ruwan dare.
Wannan gwamnati ta zama hangen dala ba shiga birni ba, duk wani Abu da akayi zaton samu daga gareta ya zama tatsuniya, saboda shugaba buhari bai samu mashawarta da makusanta na kirki ba masu kaunar al'umma illa iyaka dai suna gyara rayuwar su ne data masoyansu, shi kuma yaki ganewa. Kuma da alama haka zata kare.
Kamin kaci gaba da Karatu KASANCE DAMU A FACEBOOK: - Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update
Idan muka kalli yadda lamura suke tafiya babu wani Abu na ci gaba da za'a nuna Wanda aka samu a wannan gwamnati illa kalilan Wanda kuma ba haka akayi zato ba, duk Wanda ya zabi buhari yayi tunanin samun saukin rayuwa da magance matsaloli amma ina abin sai muni yake karawa, idan aka duba harkar:-1. Tattalin arziki ya ruguje mutane sun shiga kuncin rayuwar yau da kullum, rayuwa ta zama barazana ga kusan kowa.
2.Harkar lafiya babu canji ko kadan, babu wani tallafi a cikinta
3.Harkar ilimi abin sai kara cabewa yake.
4.Harkar samawa mutane aikinyi babu.
5. Tsarin Daukar aiki ya zama sai mai uwa a gindin murhu, maraya baya samun aiki.
6.Batun cin hanci da satar kudin gwamnati sai abin da yayi gaba, babu wani canji.
7. Bashi yana Neman danne kasar da sunan rays kasa amma babu abin a zahiri
8 Uwa uba tsaron da ake tutiya dashi yazama labari yanzu kusan kowace jaha tana fuskantar matsala.
Matsaloli gasu nan barka tai, mutane sunyi hakuri har na shekara biyar kullum ana tunanin samun sauki amma babu Alama, to ta yaya za'a ce baza'ayi ihu ba.
Abin takaici kuma mukarabbansa basu fadin gaskiya yanzu haka naji Garba shehu a BBC Hausa yana kare ihun da akayi mai makon su maida hankali akan cewa lalle ihun nan akwai dalili da Matsala, su nemi hanyar gyara amma ina sai kokarin kare kai. A magana ta gaskiya idan har ba'a tashi tsaye anyi gyara ba na zahiri Wanda mutane zasu gani su gamsu, to da alama ihu yanzu aka fara kuma abin bazaiyi kyau ba zai zama anyi karkon kifi kenan, Wanda har yanzu bamu fatan haka.
Idan kuma ance zagon kasa akewa gwamnati yo suwaye masu zagon kasar? Ba mutane bane, ina masu leken asirin kasar? Su binciko su mana a hukunta su, ko kuma basu kamuwa ne? Idan kuma ance matsalolin sunyi yawa to dama ba a shirya bane? Gaskiya a kwai sake wallahi a tashi a gyara tunda akwai Dan lokacin daya rage idan kuma akayi kememe ana zaton komai na tafiya daidai, to tabbas akwai ranar da za'ayi Dana sani wadda bata da amfani. NIDAI IYAKACINA FADI KUMA NA FADI.
Musa Ibrahim Daura
13-2-2020.
Tags:
Daga marubata