@Ma'asumah Nigeria News Updates.
17/2/2020
Wani ma’aikacin yawon bude ido a kasar Afrika ta Kudu ya dauki hoton wani biri yana renon dan karamin zaki a wani wajen shakatawa a Kruger.
Mutumin ya bayyana cewa ba a ji motsin dabbobin ba tun lokacin da aka dauki hoton a makon da ya gabata.
Wata sanarwa da mutumin mai suna Kurt Schultz ya aikawa BBC, darakta na wajen shakatawar na Kurt Safari, ya bayyana cewa yanayi na damina ya sanya ba a iya gano dabbobin ba.
Wannan hoto dai ya ja hankalin mutane da dama. Mr Schultz ya ce jaririn zakin wanda birin ya sace na cikin hadari.
Nan Biri ne Sankame da Zaki |
“Birin na tsalle-tsalle daga reshen wannan bishiyar zuwa waccan dauke da jaririn zakin na lokaci mai tsawo. Da alamu jaririn zakin ya jigata duk kuwa da cewa ba a ga alamun wani ciwo a jikinshi ba, amma akwai yiwuwar yaji ciwo a cikin jikinshi.
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
“Na taba gani biri ya kashe jaririn damisa, kuma na ga ya kashe jaririn zaki, amma ban taba ganin biri ya nunawa dan zaki irin wannan kulawa ba.”Mr Schultz ya bayyana cewa akwai yiwuwar jaririn zakin bai zai rayu ba.
Tare da wakilinmu:
Auwal M Tukur
Daga kamfanin dillancin labarai na jaridar Hausa .
Tags:
Labaran Duniya