SARKI SUNUSI :: AREWA ZA TA RUSA KANTA IDAN BA TA CANZA BA


Cikin jawabin da jaridar The Cable, ta ruwaito Sarki Muhammadu Sanusi II yana cewa, Arewa za ta rusa kanta idan ba ta canza ba. Sarkin ya yi maganar ce a a gidan gwamnatin Jihar Kaduna a jiya Litinin wurin bikin taya Gwamna Nasir El-Rufa'i murnar cika shekara 60 a duniya.

Jaridar ba ta yanko abin da Arewar za ta canza a kai ba kai tsaye daga bakin Sarkin, amma dai ta ce Sanusin ya ce: "Ba zai yiwu sauran yankunan qasar nan su yi ta zuba jarinsu a kan harkar ilimi, suna ilmantar da 'ya'yansu, suna samar da masu digiri, sannan kuma su zura mana ido da sunan ba za su samu aiki ba don sun fito daga jihar da guraben aikinta suka cika alhali mu ba mu yi wa yaranmu tanadin ilimi don gobe ba."

Sarkin kano sunusi

Na karanta labarin, na kuma sake karantawa, amma na kasa gane me Sarki yake qorafi a kai in banda kira wa Arewa bala'i kamar yadda ya saba. Da alamu shi dai a rayuwarsa bai da wani abin cewa face Arewa za ta rushe idan ta yi kaza, ko za ta tarwatse idan ta qi yin kaza. Ya manta cewa salatin Annabin da dattawan qwarai ke yi ba zai bari Arewa ta yi mummunan qarshe ba.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 



Shin yanzu za a iya cewa 'yan Arewa ba sa karatun digiri? A duba jami'o'inmu a gani mana. Ko kuwa almajiran da Sarki ke hange ne in an zo wucewa da shi suke sa shi ganin kamar matasanmu ba sa karatu? Me zai hana Sarki ya sa a qirga masa adadin masu digirin da ba su da hanyar aiki a Jihar Kano kawai don ya gane dawar garin?

Sannan wace gidauniya Sarkin ya kafa wacce za ta riqa daukar nauyin marasa galihu ga karatun na digiri kamar yadda Kwankwaso ke yi duk da babu gwamnati a hannunsa? Me ya sa Sarki Sanusi yake jin dadin yawan kushe yankinsa da mutanensa ne? Laifin me suka yi masa haka?

Muhammad Bin Ibrahim
18/02/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post